Jam’iyyar NNPP da APC sun samu nasara a zaɓen cike gurbi na jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar.
Da yake sanar da sakamakon da misalin karfe 12:36 na daren Lahadi, Jami’in zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), mai kula da mazaɓar Bagwai/Shanono, Farfesa Hassan Adamu Shitu, ya bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP, Dr. Ali Hassan Kiyawa a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri’u 16,198 kan Ahmad Muhammad Kadamu na APC, wanda ya samu kuri’u 5,347.
- Me Ya Sa Ciwon ACL Ya Zama Barazana Ga ‘Yan Wasan Kwallo?
- Zaɓen Cike Gurbi: Jauro APC Ne Ya Lashe Kujerar Ganye Ta Adamawa – INEC
Har ila yau, da misalin karfe 6:10 na safiyar Lahadi, jami’in zaɓe na INEC mai wakiltar Ghari/Tsanyawa, Farfesa Muhammad Waziri, ya bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Garba Ya’u Gwarmai a matsayin wanda ya lashe zaɓen da kuri’u 31,472 inda ya doke Yusuf Ali Maigado na NNPP, wanda ya samu kuri’u 27,931.
An gudanar da zaɓen ne bayan da INEC ta ayyana zaɓen a baya a matsayin wanda bai kammalu ba.
LEADERSHIP ta ruwaito a ranar Asabar cewa, jam’iyyar APC ta yi watsi da yadda zaɓen ya gudana, inda ta bukaci a soke zaɓukan biyu bisa zargin tayar da tarzoma daga ayyukan ‘yan daba.
Kiran ya sa shugabannin NNPP suka gudanar da zaman dirshan a ofishin tattara sakamakon zaɓen, inda suka zargi hukumar da yunkurin yin magudi a mazaɓar Ghari/Tsanyawa.
Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa wanda ke cikin shugabannin NNPP, ya tabbatar da cewa ‘ya’yan jam’iyyar ba za su fice daga cibiyar tattara sakamakon zaɓen ba har sai an bayyana sakamakon a hukumance.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp