ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Sa Ciwon ACL Ya Zama Barazana Ga ‘Yan Wasan Kwallo?

by Abba Ibrahim Wada
11 months ago
ACL

Ciwon Anterior Cruiciate Ligament (ACL) wani bangaren gwiwar mutum ne da ke hade kasusuwan gwiwar tare da haddasa motsi. Idan ACL ya samu rauni, hakan na iya janyo zafi da kumburi, sannan mutum zai rasa karfi a gwiwa – lamarin da zai sa mutum ya kasa dora nauyi a kafar ko ya iya yin wani abun motsa jiki kuma hakan ba karamar matsala bace mAmurkamman ga masu motsa jiki ko yan wasa.

Akwai abubuwa da dama da suka fi haddasa ciwon ACL mAmurkamman a kwallon kafa, abubuwan sun hada da sauya motsin jiki da sauri cikin wasa ko kuma yadda ‘yan wasa ke sauka bayan yin tsalle. Idan ACL din dan wasa ya yage kadan ko ya tsinke gaba daya, zai iya jinyar tsawon lokaci da zai iya kai wa kakar wasa guda, domin yana bukatar kulawar watanni shida zuwa tara.

  • Sin Ta Bukaci Japan Da Ta Yi Karatun Baya Game Da Batutuwan Tarihi Da Suka Shude Irinsu Batun Wurin Bauta Na Yasukuni
  • Hadin Tuwon Dawa

A wasu lokuta ma jinyar na iya fin haka dadewa kamar yadda Tyrone Mings da Emiliano Buendia suka yi jinyar fiye da shekara guda a lokacin da suka samu ciwon ACL kungiyoyin da suke bugawa wasa. Amma a halin yanzu ma akwai yiwuwar ‘yan wasan Ingila James Maddison da Lebi Colwill ba za su buga gasar Premier ba wadda za a fara a gobe Asabar sakamakon wannan raunin na ACL da suka samu a lokacin da suke buga wasannin sada zumunta a kungiyoyinsu na Tottenham da Chelsea.

ADVERTISEMENT

Sai dai a wasu lokutan ‘yan wasa ba sa iya dawowa ganiyarsu saboda tsananin ciwon da suka tsoron sake, domin yin jinyar kAmurkan shekara daya ko kAmurka da haka tana taba tunanin ‘yan wasa inda daba baya ma wasu ‘yan wasan sun afara fitar da rai daga ci gaba da buga kwallo ko kuma idan sun warke sun koma fili sun ci gaba da buga wasa basa sakin jiki su yi abin da suke yi a baya saboda tsoro.

Masana sun ce warkewa daga ciwon ya danganta da shekarun dan wasa da tsananin ciwon da kuma yadda jikin dan wasan yake bayan yi masa tiyata. Ben Warburton – likitan gashin kashi wanda yana da sabo da ciwon ACL, sakamakon aiki a kungiyar wasan Rugby na Cardiff City da kungiyar Scarlets da kuma tawagar wasan Rugby na Wales ya ce dan wasa na bukatar akalla wata shida bayan tiyata kafin ya koma buga wasa.

LABARAI MASU NASABA

Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

Ya ce idan aka yi wa dan wasa tiyata, an shafi abubuwa da yawa a cikin gwiwar saboda haka idan wadannan abubuwan suka warke, dole a bi a hankali tsawon watanni uku. Bayan nan za a iya atisaye sannan a zo batun dawowa ganiya da atisaye, da kuma dawo da karfin kafa da kuma yin guje-guje da kuma buga wasanni. Shi ya sa yake daukar lokaci kafin a koma daidai.

Warburton ya ce ‘yan wasan da suka dawo wasa wata shida bayan tiyatar ACL sun fi yiwuwar sake jin ciwon fiye da wadanda suka kwashe watanni tara. A cewarsa za a iya yin wasa ma kafin wata shida ya cika, amma dai caca ce kuma ba kowane likita bane zai bayar da shawarar yin hakan, amma dai ana yi kuma a samu nasara amma wannan babban caca ce ta gaske.

Ya ci gaba da cewa a wasu lokutan da dama ana duba dan wasa, idan dan wasa ne mai matukar muhimmanci a kungiya za a fi yin sauri da shi. Idan matashi ne tun da yana da lokaci a gaba, za ka ba shi akalla wata tara domin ya warke ya samu damar dawowa ba tare da fargabar a gaba zai sake samun irin ciwon ba saboda ciwon yana iya dawowa idan aka yi Rashin sa’a.

Shekara 10 da ta wuce, ciwon ACL yana tilasta wa ‘yan wasa yin ritaya, amma Warburton ya ce a zamanin yanzu, ‘yan wasan da aka yi musu tiyata na da yiwuwar kashi 90 zuwa 95 cikin 100 na dawowa domin ci gaba da buga wasa kuma hakan ya faru ne saboda ci gaban fasaha da bincike na taimakawa wajen kula da ciwon ACL, mAmurkamman salon yin tiyata da zaman jiyya.

Likitoci na da sababbin kayan aiki da salon aiki na yin tiyatar ACL, ciki har da yin amfani da kashin gudunmawa da wasu bangarori ma sannan akwai gwaji da yawa da likitoci suke yi wa ‘yan wasa da a baya, kamar shekara 10 da suka gabata babu fasahar yin su, hakan ya taimaka wajen sanin irin tiyatar da za a yi wa dan wasa da kuma tsawon lokacin da zai dauka yana jiyya.

Akwai yiwuwar sake jin ciwon ACL bayan tiyata cikin watanni 12 na farkocbayan dawowa yin wasa saboda ‘yan wasan suna dawo wa ne kuma kulawarsuczai ragu sannan su a rika atisaye da buga wasanni da yawa. Wasu lokutan suna rasa karfin kafarsu kuma akwai gajiya saboda haka dole dan wasa ya yi a hankali a watanni shida zuwa shekara daya na farko bayan dawowa.

Idan aka wuce wannan lokacin to babu matsala da yawa”.

Bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar sau biyu zuwa shida cewa maza za su ji ciwon ACL fiye da mata. Saboda a shekarar 2022 ‘yan wasan Arsenal Leah Williamson da Beth Mead da Bibianne Miedema sun ji ciwon ACL kuma har yanzu ana binciken dalilin da ya sa mata suka fi jin ciwon amma ana tunanin yanayin jikinsu na taka rawa. A farkon shekarar 2025 hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta bayar da kudin bincike domin gano idan al’adda na iya shafar yiwuwar jin ciwon ACL a mata.

ACL
Abba Ibrahim Wada
Website |  + postsBio
  • Abba Ibrahim Wada
    Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu
  • Abba Ibrahim Wada
    Ko Ka San Dalilin Da Ya Sa Chana Da Indiya Ba Sa Buga Kofin Duniya?
  • Abba Ibrahim Wada
    Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji
  • Abba Ibrahim Wada
    Lampard Zai Ci Gaba Da Zama A Coventry City

MASU ALAKA

Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare
Wasanni

Harry Kane: Lashe Kofin Duniya Ya Fi Mini Muhimmanci Fiye da Takalmin Zinare

July 11, 2026
Wasanni

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

July 11, 2026
Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira
Wasanni

Kofin Duniya: Na fi Son Faransa Ta Kara Da Argentina A Wasan Ƙarshe A Kan Ingila — Vieira

July 10, 2026
Next Post
Zaɓen Cike Gurbi: Jauro APC Ne Ya Lashe Kujerar Ganye Ta Adamawa – INEC

Zaɓen Cike Gurbi: Jauro APC Ne Ya Lashe Kujerar Ganye Ta Adamawa - INEC

LABARAI MASU NASABA

NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli

NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli

July 12, 2026
2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Amince Da Jamilu Gwamna A Matsayin Gwamnan Gombe

2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Amince Da Jamilu Gwamna A Matsayin Gwamnan Gombe

July 12, 2026
NDLEA Ta Gargaɗi Masu Sana’ar Keke NAPEP Kan Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

NDLEA Ta Gargaɗi Masu Sana’ar Keke NAPEP Kan Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

July 12, 2026
inec

2027: INEC Ta Tsawaita Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara

July 12, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina

July 12, 2026
Annalena Baerbock: Kasar Sin Babbar Mai Goyon Bayan Tsarin Mabambantan Bangarori Ce

Annalena Baerbock: Kasar Sin Babbar Mai Goyon Bayan Tsarin Mabambantan Bangarori Ce

July 11, 2026
Sin Ta Kalubalanci A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Kalubalanci A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya

July 11, 2026
Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

July 11, 2026
Babban Jami’i: Nazartar Mahangar Xi Jinping Mabudi Ne Na Fahimtar Kasar Sin Ta Zamani

Babban Jami’i: Nazartar Mahangar Xi Jinping Mabudi Ne Na Fahimtar Kasar Sin Ta Zamani

July 11, 2026
Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.