Tun daga watan Maris na shekarar 2021 zuwa yanzu majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, da zaunannen kwamitin majalisar, sun zartar da dokoki har 35, da yiwa wasu 62 kwaskwarima, da amincewa da kudurori 34, matakan da suka kasance tushen ingiza bunkasar kasar.
Mataimakin babban sakataren zaunannen kwamitin majalisar ta NPC Song Rui ne ya bayyana hakan a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira, don fayyace ci gaban dimokaradiyya mai salon gurguzu da aka samu a kasar Sin, yayin da ake gudanar da shirin raya kasa na shekaru biya-biyar karo na 14 tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025.
Song ya kara da cewa, wannan yunkuri na majalisar ya karfafa tsarin gudanar da gwamnati, ya kuma biya bukatun al’umma na kyautata rayuwa da karfafa tsarin tsaron kasa.
A wani ci gaban kuma, yayin wannan taro, mataimakin shugaban hukumar lura da harkokin mabanbantan kabilu na kasar Sin Duan Yijun, ya sanar da cewa, jimillar GDPn jihohi masu zaman kansu na kasar Sin, ya karu daga yuan tiriliyan 6.01, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 843.06 a shekarar 2020 zuwa kusan yuan tiriliyan 8.38 a shekarar 2024 da ta gabata. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp