Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya jinjinawa gwamnatin tarayya da jami’an tsaro bisa nasarar kama manyan shugabannin ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru da aka daɗe ana nema. A cewar ofishin jakadancin, wannan ci gaba na nuna aniyar gwamnati a yaƙin da take yi da ta’addanci a sassan ƙasar.
Tun a ranar Asabar ne gwamnatin Nijeriya ta sanar da cafke wasu jiga-jigan Ansaru da ake zargi da kitsa harin gidan yarin Kuje a shekarar 2022, wanda ya baiwa ɗaruruwan fursunoni, ciki har da ƴan ta’adda, damar tserewa.
- Gwamna Zulum Ya Bai Wa Jami’ar Sojoji Tallafin Naira Miliyan 100
- ‘Yansanda Sun Gano Nakiya A Wata Gona A Jihar Borno
A wani saƙo da ofishin jakadancin ya wallafa a shafin X, ya bayyana sunayen waɗanda aka kama da suka haɗa da Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a) da Mahmud al-Nigeri (Mallam Mamuda), yana mai bayyana cewa wannan babban nasara ce da za ta ƙarfafa gwuiwar ƴan Nijeriya a yaƙin da ake yi da ta’addanci.
Haka kuma, ofishin ya jaddada cewa wannan mataki na tabbatar da jajircewar gwamnati da hukumomin tsaro wajen kawo ƙarshen ta’addanci tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp