Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya ce babu batun yin haɗin gwiwa tsakanin Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kafin zaɓen 2027.
Yayin hira da gidan talabijin na Channels, Galadima ya zargi gwamnatin Tinubu da cin amanar Kwankwaso da NNPP a Kano, ta hanyar mara wa tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, baya duk da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige shi ta hanyar doka.
- Manoma Na Neman Ɗauki Bayan Ambaliya Ta Lalata Gonakin Shinkafa A Kebbi
- Dole Ne A Nace Kan Manufar Sin Daya Tak Don Kiyaye Zaman Lafiya A Mashigin Taiwan
“Ta yaya Kwankwaso zai yi abota da APC alhali suna yi mana haka a Kano? Sun kafa sarakuna biyu a gari guda; na Gwamnatin Tarayya da na Gwamnatin jiha. Wa ke da ikon naɗa Sarki da biyan albashinsa?” in ji Galadima.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na kare Aminy Ado Bayero ta hanyar samar masa da jami’an tsaro yayin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a wasu yankuna na Kano.
“Sun bai wa Sarkinsu (Aminu Ado Bayero) motocin ‘yansanda kusan 40 cike da jami’an Mopol, amma a wasu wurare a Kano ana kashe mutane, ana ƙwace musu wayoyi, amma ‘yansanda sun maƙale a waje ɗaya. Wannan ai abin kunya ne,” in ji shi.
Galadima, ya tabbatar da cewa NNPP za ta taka muhimmiyar rawa wajen fitar da shugaban Nijeriya a 2027.
“Mu ne za mu yanke wanda zai zama shugaban ƙasa a 2027,” in ji shi, yana mai ƙaryata batun cewa Kwankwaso zai yi sulhu da Tinubu.
Ya ƙara da cewa: “Kar wani ya fito ya ce Kwankwaso zai shiga APC. Idan an nemi yin hakan zan sani. Kwankwaso ɗaya ne daga cikin manyan ‘yan siyasa a Nujeriya yanzu, ya ƙalubalanci APC a Kano ya kuma kayar da su.”
Rigimar sarautar Kano ta ƙara dagula siyasar jihar.
A shekarar 2014, Muhammadu Sanusi II ya zama Sarkin Kano bayan rasuwar marigayi Ado Bayero.
Amma a 2020, tsohon Gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya tsige shi, ya naɗa Aminu Ado Bayero.
A watan Mayun 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya dawo da Sanusi II, lamarin da ya jawo Aminu Ado Bayero ya tafi kotu.
Tun daga wannan lokaci aka jibge jami’an tsaron tarayya a fadar da Aminu Ado Bayero ke zaune duk da cewa an tsige shi.
Galadima, ya ce Gwamnatin Tarayya na goyon bayan Bayero ne kawai saboda siyasa.
“Suna tunanin zai taimaka musu a 2027, amma babu wani Sarkin Kano da ya taɓa tantance wanda zai zama shugaban ƙasa,” in ji shi.
Jihar Kano ce ke da mafi yawan masu kaɗa ƙuri’a a Nijeriya.
A zaɓen 2023, ta kaɗa kusan ƙuri’u miliyan 1.7.
Kwankwaso ya fi kowa samu ƙuri’u, inda ya samu 997,279, Tinubu ya samu 517,341, Atiku Abubakar ya tashi da 131,716, yayin da Peter Obi ya samu 28,513.
Duk da cewa Kwankwaso ya zo na huɗu a zaɓen shugaban ƙasa da ƙuri’u miliyan 1.49, NNPP ta lashe zaɓe a ƙananan hukumomi 38 daga 44 a Kano, lamarin da ya nuna tasirinta a Arewa.
A halin yanzu, Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP ne ke mulkin jihar, amma APC na riƙe da kujeru biyu daga cikin uku na Sanata a Kano, abin da ke nuna cewa za a kai ruwa rana a zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp