A ranar Talata ne Rasha ta mayar da gawarwakin sojojin Ukraine 1,000 da ta ce 5 daga cikinsu sun mutu ne yayin da take tsare da su, kamar yadda wata hukumar gwamnatin Ukraine ta bayyana.
A nata bangaren kuma, Ukraine ta mayar da gawarwakin sojojin Rasha 19 a musayar fursunoni da ake yi.
- ‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
- Tinubu Ya Ci Amanar Kano, Babu Batun Haɗin Guiwa Tsakaninsa Da Kwankwaso A 2027 – Galadima
Dubunnan sojoji ne aka kashe daga kasashen biyu tun bayan da Rasha ta mamaye makwabciyarta a watan Fabrairun 2022.
Musayar fursunonin yaki da kuma bayar da gawarwakin sojojin da suka mutu na daya daga cikin yarjejeniyar da kasashen biyu ke aminta da ita tun bayan fara yakin.
Bangarorin biyu sun zafafa wannan kokari a ‘yan watannin da suka gabata biyo bayan wata tattaunawar sulhu a Istanbul.
“A cewar bangaren Rasha, an mayar da gawarwakin sojojin Ukraine 1,000 zuwa Ukraine,” in ji hedikwatar kula da fursunonin yaki na Ukraine a cikin wata sanarwa ta Telegram.
Zelensky ya dage cewa, dole ne Rasha ta kawo karshen yaki kafin ya amince da tattaunawar sulhu da Trump yake yi da Putin na Rasha.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp