Gwamnatin jihar Xizang mai cin gashin kai ta kudu maso yammacin kasar Sin, za ta shigar da karin makudan kudade har yuan biliyan biyu, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 280.4, domin gudanar da sabbin ayyuka 10 na kyautata rayuwar al’ummun jihar.
Sabbin ayyukan za su karkata ga fannonin bunkasa samar da kudaden shiga, da na kiwon lafiyar yara, da kula da tsofaffi, da bunkasa ayyukan kula da lafiya, matakin da zai kasance kari kan yuan biliyan 14.8 da gwamnatin jihar ke amfani da su wajen gudanar da ayyuka 28 a shekarar nan ta 2025.
Tun daga shekarar 2021, kaso sama da 80 na kasafin kudin Xizang na karkata ne ga ayyukan samar da walwala ga jama’a, inda adadin kudaden inganta rayuwar jama’a a jihar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024 ya kai yuan biliyan 860.1. A shekarar 2024 kadai, adadin kasafin jihar a fannin inganta rayuwar jama’a ya kai yuan biliyan 245.5, adadin da ya kai kaso 84 bisa dari na jimillar kasafin kudinta baki daya. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp