A ranar 18 ga watan Agustan nan ne agogon kasar Rasha, aka gudanar da bikin cudanyar al’adu mai lakabin “Sautin zaman lafiya” wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da ofishin jakadancin kasar Sin da ke Rasha suka shirya a birnin Moscow.
Daraktan CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yakin tirjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japanawa da kuma yaki da mulkin danniya a duniya.
Ya ce, a duniyar yau mai cike da rudani da cudanya da juna, muna bukatar mu zakulo hikima da abin da zai karfafa mu daga tarihi, kuma mu yi aiki tare domin tinkarar kalubale na gama-gari. CMG na son zurfafa hadin gwiwa tare da abokan huldar kasa da kasa, da gina wani dandalin watsa labarai domin bayar da rahotanni, musayar bayanai, da bai wa juna albarkatu don hada kai da fuskantar kalubale tare, da kuma neman ci gaba na bai-daya ta hanyar hadin gwiwa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp