Gwamnatin jihar Adamawa ta hada wasu yara 14 da iyayensu da aka ceto kwanan nan daga wata kungiyar safarar mutane zuwa jihar Anambra.
Mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa Farauta a yayin bikin mika yaran a ofishinta a ranar Talata, ta nuna damuwarta kan yadda jihar Adamawa ke gaba-gaba a jerin jihohin da annobar satar kananan yara ta fi kamari.
- CMG Ya Yi Bikin Cudanyar Al’adu Mai Taken “Sautin Zaman Lafiya” A Nairobi
- NNPP Za Ta Iya Goyon Bayan Takarar Tinubu A 2027 – Sakataren Jam’iyyar
A cewarta, gwamnatin jihar ta samu rahotonnin bacewar kananan yara a watan Yuli, 2025.
Ba tare da bata lokaci ba, gamayyar jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike wanda hakan ya kai ga kama wata muguwar shugabar masu safarar mutane, Ngozi Abdulwahab, mace mai matsakaiciyar shekaru.
A cewarta, Ngozi, wacce ake zargi da wannan kazamin aiki, ta kware wurin safarar kananan yara masu shekaru 4 zuwa 9 daga al’ummomi daban-daban na jihar zuwa yankin kudu maso gabashin Nijeriya, inda ta ke sayar da duk yaro daya kan kudi tsakanin ₦800,000 zuwa ₦1.7 miliyan.
Domin boye mummunar sana’arta, wacce ake zargin tana kasuwanci ne a wani dan karamin kanti inda take sayar da kayan kwalama a unguwar Jambutu da ke karamar hukumar Yola ta Arewa wajen karkatar da hankalin yaran.
Yaran da aka ceto sun hada da Fatima Husseini, Nusaiba Abdulaziz, Maimuna Ibrahim, Ibrahim Hamman, Ismail Mohammed Iliyasu Umar Mohammed da Umar Mohammed.
Sauran sun hada da Nana Khadija Abdulwahab, Dahiru Abdulwahab, fatima Ismail, Muhammad Buba, Umar Farouk, Muhammad Abubakar, Nana Khadija da Suleiman Saleh.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp