Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Yamma, Ahmed Wadada, ya fice daga jam’iyyar SDP, mako guda bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu.
A ranar 13 ga watan Agusta, bayan ziyarar da ya kai fadar shugaban ƙasa, Wadada ya shaida wa ‘yan jarida cewa babu wani ɗan takara daga jam’iyyar hamayya ta ADC da zai iya yin aiki sama da Shugaba Tinubu.
- Xi Jinping Ya Halarci Bikin Cika Shekaru 60 Da Kafuwar Jihar Xizang Mai Cin Gashin Kanta
- Kura Za Ta Ce Da Kare Maye
Wadada ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar a cikin wasiƙar da ya aike wa shugaban SDP na Tudun Kofa, a ƙaramar hukumar Keffi, Jihar Nasarawa.
A cikin wasiƙar, ya ce ya ɗauki wannan mataki ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar, wanda ya haddasa rabuwar kawuna.
Ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta ba shi amma ya ce lokaci ya yi da zai ɗauki wata tafiyar.
Har yanzu, Wadada bai bayyana wacce jam’iyya zai koma ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp