’Yan Nijeriya biyu Collins da Osas, an ruwaito sun rasu a birnin Tripoli, babban birnin kasar Libya, mutuwar da ake zargin tana da alaka cin guba, kamar yadda PUNCH Metro ta wallafa. Wakilinmu ya nakalto a ranar Asabar, cewa wadanda abin ya shafa, wadanda duk suna zaune a yankin Misrata ta kasar, sun yi tafiya zuwa Tripoli a ranar 20 ga Yuli tare da wani aboki da ba a bayyana sunansa ba.
“Wata majiya daga dangin marigayi Collins, ta shaida wa PUNCH Metro cewa a ranar Asabar cewa an ce abokin ya bar su a can ya koma Misrata shi kadai, daga baya ya samu kiran waya cewa abokan tafiyarsa biyun sun rasu bayan zargin an basu guba.”
- Hukumar Kwastam Ta Kama Kayan Maye Na Miliyan 680 A Katsina
- Dalilin Da Ya Sa Gwamnatin Jihar Kuros Ribas Ta Yi Hadaka Da Hukumar NPA
“An shaida mana cewa su uku suna zaune a Misrata, sannan dukkansu suka yi tafiya zuwa wani wuri da ake kira Oshofana a Tripoli domin shakatawa. Ko da yake Collins da Osas ba su saba da wurin ba, shi ne karo na farko da suka je can. An ce wuri ne da ake gudanar da kasuwanci iri-iri.”
“Don haka, bayan sun kwana hudu a can, abokin da suka bi zuwa wurin ya ce zai koma Misrata, amma Collins da Osas suka ce za su ci gaba da zama a wurin. Sai ya bar su a wurin ya koma. Bayan kusan kwanaki biyu ne ya ce ya samu kiran waya cewa abokan aikinsa biyun sun rasu ana zargin guba aka basu a abinci,” in ji majiyar.
“Wata majiya cikin kasar ta shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce tun tuni.”
Labarin abokinsu da ya bayar bayan ya dawo gida ya haifar da zargi.
“A sanin da muka yio wa Oshofana, labarin mutumin da suka bi zuwa wurin dole ya haifar da zargi. Wannan shi ne abin da ya gaya mana domin babu wanda ya tafi tare da su. Amma wasu daga cikin abokan aikimu nan ba su gamsu da bayaninsa ba, suna kuma bin diddigin binciken da ake yi domin gano musabbabin mutuwarsu,” in ji majiyar.”
Majiyar ta kara da cewa an riga an binne abokan da suka rasu a cikin kasar.
Da aka tuntubi mai magana da yawun Hukumar ‘Yan Nijeriya mazauna kasashen waje, Abdulrahman Balogun, ya ce bai da masaniya kan lamarin.
Ya ce, ‘Ban san da lamarin ba, amma iyalansu na iya rubuta korafi zuwa gare mu a matsayin hukuma, kuma za mu yi aiki a kai.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp