Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin cafke da kuma hukunta masu hannu a kisan da aka yi wa wasu masallata a Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wannan hari a matsayin “hari ne na rashin imani da ta’addanci,” tare da jaddada cewa ba zai wuce ba tare da hukunci ba.
- Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe
- Manyan Jami’an JKS Sun Ziyarci Jami’ai Da Mazauna Birnin Lhasa
Ministan ya ce jami’an tsaro suna kan bin sawun ‘yan ta’addan, tare da tabbatar da cewa “ba za a bar wata kafa ba sai an kama su, kuma an hukunta su yadda ya dace.”
Ya ƙara da cewa: “Gwamnati tana tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa adalci zai kasance cikin gaggawa kuma mai ƙarfi, kuma ba za a taɓa bari irin waɗannan ayyukan ta’addancin su samu gindin zama a ƙasar nan ba.”
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan, al’ummar Malumfashi da kuma Gwamnatin Jihar Katsina.
Idris ya ce: “Damuwa da ɓakin cikin su namu ne, kuma gwamnati tana tare da su a wannan lokaci mai duhu. Allah Maɗaukaki ya jiƙan waɗanda suka rasu, ya kuma bai wa waɗanda suka rage ƙarfin zuciya da juriyar ɗaukar wannan babban rashi.”
Ministan ya kuma jaddada nasarorin da ake samu kwanan nan a yaƙi da ta’addanci, inda ya bayyana cewa Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) ta cafke manyan shugabannin ƙungiyar ta’addanci ciki har da Mahmud al-Nigeri na ƙungiyar Mahmuda, da mataimakin sa Abu Abba, da kuma Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a) na ƙungiyar Ansaru – waɗanda dukkan su suna cikin jerin masu laifi da ake nema a duniya.
Ya ce: “Wannan kama manyan shugabannin ya nuna irin nasarorin da ake samu a cikin ayyukan yaƙi da ta’addanci a ƙasar nan, bisa umarnin Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda ya bayyana a sarari cewa ayyukan ta’addanci da ke barazana ga Nijeriya da ‘yan ƙasa nan ba da jimawa ba za su zama tarihi.”
Ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta taɓa barin wanda ya zubar da jinin jama’a ya samu mafaka a Nijeriya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp