Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, za ta yi amfani da harsuna guda 85, don gabatar wa duk fadin duniya bikin cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka yi nasara a yakin turje wa kutsen Japanawa da karshen yakin duniya na II, gami da gagarumin bikin faretin soja a Beijing.
Domin gabatar da rahotanni da shirye-shirye masu inganci game da bikin zuwa ga duk fadin duniya, CMG ta fara amfani da karin wasu sabbin harsuna guda uku wajen watsa shirye-shiryenta a kwanakin baya, ciki har da Irish, da Tok pisin, da kuma harshen Rwanda. Daga cikinsu, yawan masu amfani da harshen Rwanda ya zarce miliyan 13, wadanda ke zaune a kasashen Rwanda, Burundi, Uganda da kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.
Amfani da karin harsunan uku, zai fadada yankunan da ke iya karbar shirye-shirye da CMG ke gabatarwa a yammacin Turai, da kudancin yankin tekun Pasifik gami da tsakiya da gabashin Afirka, al’amarin da ya sa CMG ta ci gaba da zama babbar kafar watsa labarai dake amfani da harsuna mafi yawa a duniya wajen watsa shirye-shirye. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp