Gwamnatin Jihar Sokoto ta ƙaryata rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) da ya nuna cewa jihar ce ke da mafi yawan tsananin talauci a Nijeriya, inda ta bayyana cewa hanyar da aka yi amfani da ita wajen binciken bata wadatar ba.
Kwamishinan tsare-tsare da bunƙasar tattalin arziƙi na jihar, Dr. Abubakar Muhammad Zayyanu, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a wani taron bita na yini guda da aka shirya tare da haɗin gwuiwar UNICEF, da tarayyar turai da sauran abokan cigaba a Sokoto. Ya ce binciken na NBS da aka gudanar tun a 2022 bai nuna halin da ake ciki a yanzu ba.
- Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa ADC A Sokoto
- Man United Sun Kammala Sayen Benjamin Sesko Daga RB Leipzig
Dr. Zayyanu ya bayyana cewa gwamnatin jihar tare da kamfanin Red Wire sun gudanar da sabon bincike domin tantance matsayin talauci daga lokacin binciken NBS zuwa yanzu. Ya ce gwamna ya amince da sabon binciken domin tabbatar da sahihancin bayanai, kuma rahotannin farko sun nuna an samu wasu cigaba masu kyau.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta wallafa cikakken sakamakon binciken bayan kammala nazarin bayanan. Haka kuma ya tuna cewa a taron Majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta, an gabatar da shirin Bankin Duniya da zai duba tattalin arziƙi da yawan jama’a daga matakin gunduma.
Zayyanu ya ce gwamnatin Sokoto tana amfani da tsarin “bottom-up approach” wajen tattara bayanai daga ƙananan hukumomi da mazabu 886, domin samar da ingantattun hanyoyin magance talauci ta hanyar bayanai da aka tabbatar da sahihancinsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp