Wani matashin ɗan Nijeriya mai shekaru 17, Abdul Jabar Adama, ya lashe lambar azurfa a gasar ninkayar matasa ta duniya da aka yi a ƙasar Romania.
Wannan shi ne karon farko da Nijeriya ta taɓa samun irin wannan lambar yabo a tarihin gasar.
- An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing
- Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO
A gasar da ta ɗauki kwanaki shida, Adama ya samu lambar azurfa a tseren ninkaya na mita 50, inda ya kammala a cikin daƙiƙi 23.64.
Ya zo na biyu bayan da ɗan Birtaniya, Dean Fearn, wanda ya lashe zinariya da daƙiƙa 23.54.
Ba wai kawai ya samu lambar yabo ba, Adama ya kuma karya tarihin Nijeriya sau biyu a rana guda.
Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics.
Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara a fannin ninkaya ba.
Hukumar wasanni ta kasa ta taya shi murna, tare da hukumar kula da wasannin ruwa ta Najeriya. Darakta Janar, Bukola Olopade, a cikin sanarwarsa a ranar Lahadi, ya ce wannan babbar nasara ce ga wasannin Najeriya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp