Da safiyar yau Talata 26 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban majalisar dokokin kasar Rasha Vyacheslav Volodin a nan birnin Beijing.
Yayin tattaunawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, a mako mai zuwa, Sin za ta gudanar da bikin tunawa da cika shekaru 80 da cin nasarar yakin kin maharan Japan, da kuma yaki da tafarkin murdiya. Sin da Tarayyar Soviet, a matsayin manyan fagagen yaki na Asiya da Turai bi da bi, sun yi babbar sadaukarwa don yakar mamayar dakarun Japan, da kuma mamayar sojojin Facist na Jamus, kuma sun ba da gudunmawar da ta kai ga cimma nasarar yakin duniya na biyu.
Shugaba Xi ya kara da cewa, ya kamata bangarorin biyu su ci gaba da kara karfafa abota, da zurfafa amincin manyan tsare-tsare, da kara hadin gwiwa a fannoni daban-daban, tare da kare bukatunsu na tsaro da ci gabansu, dadin dadawa da hadin kai da kasashe masu tasowa, ta yadda za su rika bin ainihin manufar hadin gwiwa ta duniya, da kuma taimakawa wajen inganta tsarin duniya mafi adalci da inganci.
A nasa bangaren Volodin ya ce, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, dangantakar Rasha da Sin ta ci gaba da zurfafa cikin nasara. Majalisar dokokin Rasha ta himmatu wajen aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin dokokin kasashen biyu, da kuma himmatuwa wajen samun karin sakamako mai kyau a dangantakar kasashen biyu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp