Tsohon gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce jam’iyyarsu ta ADC tana da kyakkyawar damar kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Amaechi ya bayyana haka ne a wani taro da ya halarta a Jihar Kano tare da ‘yan kasuwa, inda ya jaddada cewa babu batun yin sulhu a jam’iyyar idan aka zo fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa.
- Tallafin Walwalar Jama’a: Yadda Gwamnatocin Biranen Kasar Sin Ke Jifan Tsuntsu Biyu Da Dutse Daya
- Yadda Aka Cafke Masu Saka Ƙwayoyi A Jakunkunan Matafiya A Filin Jirgin Sama A Kano
Ya ce kowa yana da damar tsayawa takara a ADC, kuma shi ma zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027.
A cewarsa: “Ni takarar shugaban ƙasa zan yi, ba zan janye wa kowa ba. A bar jama’a su zaɓi wanda suka fi so.”
Amaechi ya kuma caccaki Shugaba Tinubu, yana mai cewa salon siyasar sa ya gaza kawo sauƙi ga rayuwar ‘yan Nijeriya, har ma da mutanen Kudu yankin da ya fito.
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027.
Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai.
Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp