Mai magana da yawun marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya mayar da martani game da tantancewar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi wa ubangidansa, bayan rasuwarsa, inda ya bayyana cewa, babu wani abu illa kawai tsanarsa da ya yi.
Da yake mayar da martani ga sabon hukuncin da Obasanjo ya yanke kan gwamnatin Buhari (2015-2023), inda ya bayyana wa’adin mulkin a matsayin mafi muni a mulkin farar hula a Nijeriya, Shehu ya bayyana cewa; tuni ya bayyana dalilin da ya sa Obasanjo, bai taba son marigayi tsohon shugaban kasa Buhari ba a littafinsa da ya wallafa na baya-bayan nan.
- Al’umma Da Ƴan Bindiga Sun Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya A Katsina
- Bincike Ya Nuna Tarin Fuka Na Kashe Mutum 71,000 A Nijeriya Duk Shekara
Sai dai ya ce, marigayi tsohon shugaban kasar yana matukar girmama Obasanjo, inda ya kara da cewa; sun yi takun-saka ne da shi a kan wata bukata tasa da ba ta biya ba.
Shehu, a cikin littafin nasa wanda ya bai wa wakilinmu na LEADERSHIP, ya yi zargin cewa; Obasanjo ya bijiro wa Buhari da wasu bukatu a lokacin da yana shugaban kasa (Obasanjo).
Ya kara da cewa, “Akwai da dama a kusa da Buhari da ke ganin cewa; abin ban mamakin da ya faru a tsakanin Buhari da wanda ke gabansa a aikin sojan da yake mutuntawa, Shugaba Olusegun Obasanjo, shi ne sakamakon bukatar da aka ce Obasajon ya nemi a bai wa wani dan kwangila da yake so a aikin wuta ta Mambila.
“A kan haka, Buhari cikin ladabi ya fada wa tsohon shugaban kasar cewa, ya bar shi ya gudanar da abin da ya kamata, ta hanyar bin tsarin da ya dace; ba na son zuciya ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp