Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.
Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi.
- Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata
- An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki
Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, inda ya sake yi musu ta’aziyya.
ADVERTISEMENT
Ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari cewa zai ci gaba da kula da ayyukan alheri Buhari ya bari.














