Kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ta yi gargadin cewa karuwar matsalolin tsaro da talauci da kalubalen muhalli na kai al’ummar arewacin Nijeriya bango. Gargadin na zuwa ne bayan taron kwamitin zartarwa na kungiyar karo na 78 wanda ya gudana a Kaduna.
Shugaban ACF, Mamman Osuman, ya ce, arewa ba za ta ci gaba da zama shiru yayin da rayuka da dokiyoyi ke ci gaba da salwantuwa.
- Bincike Ya Nuna Tarin Fuka Na Kashe Mutum 71,000 A Nijeriya Duk Shekara
- Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah
Ya ce, “Yanzu ba lokaci ne na yin shiru ba. Tsaronmu na ci gaba da tabarbarewa, ana kwashe mana albarkatun kasa, sannan matsalolin muhalli su na karuwa. Dole ne arewa ta farka, ta tashi ta hada kai domin kare kanta,” ya shaida.
Osuman ya koka kan yadda a kowace rana ake kashe rayukan mutane a yankin, ya kara da cewa, yara, mata, maza, tsofaffi duk sun fada cikin matsalolin ambaliyar ruwa, ta’addancin ‘yan bindiga dadi, ayyukan ‘yan ta’adda da sauran annobobi.
Ya bukaci shugabannin arewa da mazauna yankin da su farka, su hada kawunansu kana su dukufa da yin addu’o’in neman zaman lafiya a yankin.
Da yake magana da kafar BBC bayan taron, mai ba da shawara ga ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, kungiyar ta yi nazari da bitar matsalolin da suke addabar arewa tare da cimma matsayar cewa akwai bukatar daukan matakan gaggawa.
“Matsalolin nan ga su nan a zahirance, kuma dole ne a tursasa gwamnati ta dauki mataki. Ba abun da ya fi damun arewa a halin yanzu kamar matsalar rashin tsaro, garkuwa da mutane da yawan kashe-kashe a ko’ina. Dole ne jama’an arewa su hada kawunansu su tilasta wa gwamnati yin abun da ya dace,” ya shaida.
ACF ta kuma nuna gayar damuwa kan rahoton baya-bayan nan da kungiyar Amnesty International ta fitar da ke cewa sama da mutane 10,000 da aka kashe a yankin arewa cikin shekaru biyu kacal na mulkin Shugaban kasa Bola Tinubu.
A cewar Gentile, kashe-kashen yana tare da yawaitar sace-sacen jama’a da kai hare-hare a kauyuka.
Kungiyar ta soki shirun da jami’an gwamnati suka yi kan binciken na Amnesty, inda ta ce kin kalubalantar alkaluman ya nuna yadda rikicin ke da tsanani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp