Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ya ce, babu wani ɗan takarar shugaban ƙasa da aka haramtawa tsayawa takara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne kwamitin tantancewa ƙarƙashin jagorancin John Oyegun, tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa ya gabatar da rahotonsa ga shugaban jam’iyyar APC.
Oyegun ya ce, kwamitin ya fito da jerin sunayen ’yan takara 13 daga cikin 23 da suka gabatar da kansu domin tantancewa.
- Gwamnonin APC Suna Goyan Bayan Osinbajo A Zaben Fidda Gwani
- ‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mahaifiyar A.A Zaura
Da ya ke magana da manema labarai a ranar Asabar, Adamu ya ce, tantancewar tamkar jarrabawa ce da ɗalibai ke fitowa da maki daban-daban.
Rahotanni sun nuna cewa, mutum 13 da ke fatan tsayawa takarar shugaban ƙasa an kasafta su cikin jerin sunayen waɗanda Oyegun ke jagoranta, yayin da sauran goman da ke fatan shugaban ƙasa ba su shiga cikin jerin sunayen ba.
Waɗanda aka sanya a cikin jerin sune Tinubu, mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo; Rotimi Amaechi, ministan sufuri; Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa; Yahaya Bello, gwamnan Kogi; Kayode Fayemi, gwamnan Ekiti, da Emeka Nwajiuba, tsohon ƙaramin ministan ilimi.
Sauran sun haɗa da Ogbonnaya Onu, tsohon ministan kimiyya da fasaha; Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan Ogun; David Umahi, gwamnan Ebonyi, Muhammad Badaru, gwamnan Jigawa; Godswill Akpabio, tsohon gwamnan Akwa Ibom; da Tein Jack-Rich, wani ma’aikacin mai.
Sauran ’yan takara 10 da ba a sanya su cikin jerin ba sun haɗa da Tunde Bakare, Rochas Okorocha, Ben Ayade, Sani Yerima, Ken Nnamani, Ikeobasi Mokelu, Demeji Bankole, Felix Nicholas, Uju Ken-Ohanenye, da Ajayi Borroffice.
Abdullahi Adamu dai ya mike haikan wajen ganin APC ta tsayar da dan takarar da zai samu karbuwa a wurin ‘Yan Nijeriya domin jam’iyyarsa ta ci gaba da jan ragamar mulkin Nijeriya a 2023.