Tun farko kafin fara yin mulkin mallaka Sarakunan gargajiya sune suka kasance tamkar ‘yan majalisa, irin na wakilai da kuma Dattawa da ake da su yanzu, lokacin ana da sassa uku da suka hada da Arewaci, Yammaci, da kuma Kudanci, an kafa sune a matsayinsu na Sarakunan gargajiyar, da kuma sauran masu tafiyar da al’ummar su a gargajiyance, saboda su samu damar yin wasu ayyuka tamkar a gwamnatance ne kafin,da kuma lokacin mulkin mallaka. Sune suka kasance kamar ‘yan majalisar Dattawa a tsarin majalisa irin na tsarin majalisa na na tsarin mulkin bicameral na Turawa, a wasu sassan Nijeriya kafin a daina yin amfani da tsarin lokacin da aka yi gyare- gyare a tsarin mulkil.
Tsarin mulkin gargajiya shi aka fara amfani da shi kafin lokacin mulkin mallaka ya bayyana ta yadda suke lura da lamurran da suka shafi aikin gona da albarkar kasa, a wasu kananan larduna ko sashe, da kuma sauran da suke ana iya kiransu da sunan Jiha daga shekarar 1400 zuwa 1800. A tarihance Sarakunan gargajiya na Arewanci da kuma Shugabannin gargajiya a sashen Kudanci suna yin ayyukan da suka shafi addini, kasance kamar kotuna,da kuma tafiyar da harkokin mulki. Zamanin mulkin mallakar da aka fi sani da indirect rule, da aka yi amfani da shi a Nijeriya inda a lokacin Sarakunan gargajiya ne, suka zama tamkar gwamnati a gargajiyance, saboda ai har ma kiransu ake da sunan natibe authorities, sun yi aiki tare a lokacin da masu saukin kai wadanda kuma su Turawan suke ma, kallon barazana ce sun raba su da mulkin tafiyar da al’ummarsu.
Kafawa
Majalaisar Sarakuna daga karshe an kafa ta ne a shekarar 1951,a karkashin tsarin mulkin Macpherson, wanda shi matufar tsarin mulkin ita ce a karawa Nijeriya kasancewa cikin tafiyar da gwamnati, yayin da shi kuma lamarin da ya shafi Sarakunan ko masarautun gargajiya aka shigar da su cikin lamarin siyasa.An kafa majalisar Sarakuna a sassa uku na Nijeriya wadanda suka hada da sashen Arewaci, Yammaci, da kuma Gabashi.Daga baya kuma an maye wancan da majalisar Sarkuna.
Watan Mayu 1956,aka gabatar da kudurin niyyar yin doka a majalisar Kudu maso gabashin Nijeriya, suka gabatar da kudurin zai bada dama ta a amince da Sarakunan gargajiya, wanda ta haka ne aka samu damar kafa majalisar Sarakunan Kudu maso gabashin Nijeriya, duk kuwa a lokacin da akwai turjiyar da aka samu daga masu fafutukar tafiyar da lamurra yadda suka dace, saboda sun ki goyon bayan a sa su masu Sarautun gargajiya a harkokin yadda ake tafiyar da gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp