Gwamnatin Jihar Kaduna ta zargi tsohon gwamna Nasir El-Rufai da shirin tayar da fitina a jihar, tare da gargadɗnsa da ya daina duk wani yunƙuri na ta da hankalin al’umma.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Dokta Suleiman Shuaibu, ya fitar, Gwamnatin ta ce al’ummar jihar sun wahala, an zubar da jininsu tare da samum rabuwar kai a lokacin mulkin El-Rufai.
Sanarwar ta bayyana cewa abubuwan da El-Rufai ke yi a kwanakin nan ba siyasa ce kawai ba, barazana ce kai-tsaye ga zaman lafiya da ci gaban jihar.
Gwamnatin ta zarge shi da ƙoƙarin jefa Kaduna cikin rikicin ƙabilanci da addini, rashin tsaro da matsalolin tattalin arziƙi.
Gwamnatin ta ce El-Rufai ba ya jin daɗin ci gaban da aka samu a ƙarƙashin Gwamna Uba Sani, wanda aka yaba da salon mulkinsa ta hanyar haɗa kan jama’a da mayar da hankali kan tsaro.
Ta ce cikin ƙasa da shekara biyu, Kaduna ta fito daga durƙushewar tsari zuwa zama jihar da ake ganin tsari.
Haka kuma, gwamnatin ta yi zargin cewa El-Rufai ya ƙara ƙoƙarin tayar da rikici bayan abokan siyarsarsa sun sha kaye a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga watan Agusta.
Ta ce sakamakon ya nuna rashin amincewa da salon mulkin El-Rufai na “rabuwar kai da wariya” tare da amincewa da salon mulkin Gwamna Uba Sani.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin El-Rufai kan waɗannan zarge-zarge, amma ba a iya samun shi ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp