Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sanar da rasuwar, Farfesa Hafiz Miko Yakasai, ƙwararren masani kuma jigo a fannin ilimin harshe, wanda ya rasu a ranar Alhamis, 4 ga Satumba, 2025, a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.
Kafin rasuwarsa, Farfesa Yakasai malami ne a Sashen Kimiyyar Harshe da Ilimin Fassara a Jami’ar BUK, kuma kwanan nan aka naɗa shi a matsayin ‘Provost’ na farko a Kwalejin Kimiyyar Ɗan’adam da aka kafa a jami’ar. Jami’ar ta bayyana wannan naɗin a matsayin “shaida ta sadaukarwarsa ga harkar ilimi da bunƙasa ilimin harshe.”
- Ɗaliban Jami’ar Bayero ‘Yan Ajin 2015 Sun Zamanantar Da Ɗakin Karatu Na M.A.Z Sani
- Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban BUK Ta Karrama Dr. Sani Dauda Ibrahim Da Walimar Kammala Digiri Na 3
A cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar, BUK ta bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi, tana cewa: “Farfesa Miko babban masani ne, haziƙin malami kuma gogaggen mai ilimi da ya bayar da gudunmawa mai tarin yawa wajen koyar da harsunan Nijeriya da fannin kimiyyar harshe.” Ta ƙara da cewa ilimi da kyakkyawan aikin da ya bari zai ci gaba da zama abin koyi ga ɗalibai da masana a yanzu da nan gaba.
Farfesa Yakasai ya shahara wajen nazarin harshen Hausa da ilim fassara. Ya taka gagarumar rawa wajen haɓaka Kamus na Turanci zuwa Hausa da kuma Hausa zuwa Turanci, inda ya taimaka wajen tsara fassara da ƙa’idojin amfani da kalmomi. Haka kuma, ya bayar da gudummawa ga Mujallar Ɗundaye ta Nazarin Harshen Hausa, kuma mamba ne a
kwamitin ‘Journal of African Languages and Literatures.’
A wajen jami’a kuwa, Farfesa Yakasai ya kasance jigo a fagen fassara ta ƙwararru, inda ya rike muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa na Farko, sannan daga baya aka naɗa shi Shugaban Ƙungiyar Fassara da Tafinta ta Nijeriya (NITI). Ya jagoranci tarukan ƙasa kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa reshen ƙungiyar a Jihar Kano a shekarar 2021.
A fannin ƙasa da ƙasa, ya kammala karatun digirinsa na uku (PhD) a Jami’ar Warsaw da ke ƙasar Poland, ƙarƙashin kulawar shahararriyar masaniyar harshe, Farfesa Nina Pawlak.
BUK ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalansa, abokansa da duk waɗanda rashi ya shafa, inda ta bayyana cewa: “A madadin Uban Jami’ar da Shugaban Jami’ar da Majalisar Gudanarwa da ta Majalisar Malaman jami’ar da Kwamitin Ma’aikata da Dalibai, muna miƙa ta’aziyyarmu ga iyalansa da dukkan al’ummar.”
Za a gudanar da sallar jana’iza a ranar Juma’a, 5 ga Satumba, da ƙarfe 9:00 na safe, a gidansu da ke Unguwar Yakasai, kusa da *
Makarantar Kwana ta Shekara da ke Kano.
Za a ci gaba da tunawa da Farfesa Hafiz Miko Yakasai a matsayin masanin ilimi mai tawali’u, wanda aikin da ya yi zai ci gaba da haskaka fannin harsunan Hausa da na Afirka baki-ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp