Kwanan baya, kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun mai da matukar hankali kan bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, wanda aka yi a birnin Beijing na kasar Sin a ranar 3 ga wata. Kana, kafofin watsa labarai da dama na kasashe daban daban sun rika amfani da kalmar “Zaman lafiya” a lokacin da suke watsa labarai kan wannan gagarumin biki.
Yakin duniya na biyu ya bakanta ran bil Adama, kuma kasar Sin ta cimma nasarar yaki da mamayar dakarun kasar Japan bayan al’ummomin kasar sun shafe tsawon shekaru 14 suna yaki, lamarin da ya ba da muhimmiyar gudummawa ga cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiya.
Bugu da kari, wani muhimmin darasi da aka koya daga yakin shi ne, dole ne a tsaya tsayin daka wajen neman ci gaba ta hanyar zaman lafiya. Haka kuma, a halin yanzu da ake fuskantar sauye-sauye a duniya, shugaba Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin kiyaye dauwamammen yanayin tsaron duniya cikin hadin gwiwa, kuma bisa dukkan fannoni, wanda hakan ya ba da amsar kasar Sin game da yadda za a warware matsalar rashin tsaro daga tushe.
Dukkanin bil Adama na fuskantar makoma iri daya, ba za mu iya shimfida zaman lafiya a duniyarmu ba, har sai dukkanin kasashe da kabilu su girmama juna, da yi wa juna adalci da kuma taimakawa juna. Ya kamata mu kawar da harkokin da za su haddasa yake-yake daga tushe, domin magance faruwar abubuwa masu bakanta rai da suka taba aukuwa a tarihi. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp