Sashen cinikayyar bayar da hidimomi na kasar Sin ya samu ci gaba mai inganci a watanni bakwai na farkon shekarar nan ta 2025, inda a cikinsa bangaren hidimomin tafiye-tafiye ya samu babban ci gaba.
Hakan na kunshe ne cikin wasu alkaluman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar ta fitar a Juma’ar nan. Alkaluman sun kuma nuna yadda darajar hada-hada a fannin na cinikayyar bayar da hidimomi ta kai kudin Sin Yuan tiriliyan 4.58, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 644.2 cikin wa’adin na watanni 7, kuma karuwar da aka samu a fannin ta kai ta kaso 8.2 bisa dari kan mizanin shekara.
Kazalika, darajar hidimomin da aka fitar ketare ta kai kusan Yuan tiriliyan 2, adadin da ya karu da kaso 15.3 bisa dari kan mizanin shekara, yayin da fannin cinikayyar hidimomin da aka shigo da su daga ketare ya kai Yuan tiriliyan 2.58, karuwar da ta kai ta kaso 3.3 bisa dari bisa mizanin shekara, tare da samar da rarar Yuan biliyan 581.56.
Fannin cinikayyar da ta shafi hidimomin tafiye-tafiye ta ci gaba sosai, inda darajarta ta karu da kaso 10.4 bisa dari zuwa Yuan tiriliyan 1.26. Yayin da bangaren hidimominta da aka fitar ketare ya karu da kaso 62.9 bisa dari. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp