Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta ba ɗan gwagwarmayar dimokuraɗiyya kuma mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, wa’adin mako guda domin ya janye wani abu da ya wallafa a shafin X (Twitter) kan Shugaba Bola Tinubu, wadda hukumar ta ce “ƙarya ce, ta ɓata suna kuma tana iya tada zaune tsaye.”
A cikin wasiƙar da DSS ta aika masa ranar 7 ga Satumba, 2025, ta zargi Sowore da yin kalaman batanci da cin mutunci ga shugaban ƙasa a wallafar da ya yi ranar 26 ga Agusta, inda ya kira Tinubu “ɓarawo” tare da zargin cewa ya yi wa ’yan Nijeriya ƙarya bayan ya ce cin hanci da rashawa sun daina wanzuwa a gwamnatinsa yayin da yake ziyara a Brazil. Hukumar ta yi gargaɗin cewa rashin bin umarninta zai tilasta mata ɗaukar duk wanivmataki na doka domin kare tsaron ƙasa da zaman lafiya.
- Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10
- Buratai Ya Bukaci Kotu Ta Ci Tarar Sowore Naira Biliyan 10 Kan Bata Masa Suna
DSS ta buƙaci Sowore da ya goge rubutun, ya sake wallafa sabuwar sanarwa a shafin X daidai da yadda ya bayyana tun farko, sannan ya buga sanarwar neman afuwa a aƙalla jaridu biyu na ƙasa da tashoshin talabijin biyu masu yaɗa shirye-shirye a faɗin ƙasa. Haka kuma ta umarce shi ya tura rubutaccen bayani zuwa shalƙwatar DSS a Abuja ko ta adireshin imel na hukumar cikin mako guda.
Hukumar ta kuma sanar da cewa ta tura kwafin wasiƙar zuwa ofishin jakadancin Amurka a Abuja, tana nuna cewa lamarin ya ja hankalin diflomasiyyar ƙasashen waje duba da matsayin Sowore na zama a Nijeriya da Amurka. Ta gargaɗe shi da cewa a matsayinsa na wanda ke neman muƙamin siyasa, dole ya nuna ƙwarewa da ladabi a magana da aiki, saboda hakan na da muhimmanci wajen inganta zaman lafiya da tsaro a ƙasar.
DSS ta nanata cewa aikinta na doka shi ne tabbatar da cewa ’yan Nijeriya ba sa samun labaran yaudara ta hanyar yaɗa ƙarya ko farfaganda, tana mai cewa idan Sowore bai janye maganarsa ba cikin wa’adin da aka bayar, to za ta ɗauki matakan da ta dace bisa doka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp