Yau 8 ga Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar bude taron tattauna harkokin ciniki da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25 (CIFIT).
Cikin sakon, Xi ya bayyana cewa, gudanar da taron na wannan karo bisa taken “kara zuba jari tsakanin bangarori 2 don habaka ci gaban duniya” zai taka muhimmiyar rawa wajen inganta tattalin arzikin duniya mai bude kofa. Ya ce taron ya zama dandamali mai inganci ga masu zuba jari na duniya su kara hadin gwiwa.
Xi ya kuma jaddada cewa, a matsayin babbar kasa mai ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya da kuma kwanciyar hankali, Sin za ta ci gaba da karfafa bude kofa mai zurfi, da inganta ‘yancin ciniki da saukaka zuba jari, da ci gaba da samar da damarmakin ci gaba ga duniya, don ba da karin ingantacciyar gudunmawa da tabbaci ga ci gaban duniya.
An bude taron CIFIT karo na 25 a yau a birnin Xiamen na lardin Fujian, wanda ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta shirya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp