Tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin, ta cimma wani sabon ci gaba a aikin kimiyyar rayuwa, wanda ke lura da yadda irin shuka daban-daban suke girma a sararin samaniya.
Samfuran nau’o’i irin shuka guda biyu, wato furen “thale cress” da shinkafa, sun kasance a dakin gwaji tun ranar 28 ga Yuli. An yi amfani da irin furen “thale cress” a zaman samfurin kwayoyi don gudanar da bincike na tushe.
Cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin (CAS) ta bayyana a wani taron manema labarai da ta kira jiya cewa, gwajin dashen “thale cress” da shinkafa da ke cikin na’urar bincike ta Wentian na kasar Sin, na ci gaba da tafiya yadda ya kamata.
Ya zuwa yanzu, furen “thale cress” ya fitar da ganye hudu. Yayin da girman nau’in shinkafa mai tsayi ya kai tsayin kusan santimita 30, kana girman nau’in gajeriyar shinkafar ta kai kusan santimita 6.
A cewar Zheng Huiqiong, wata mai bincike a cibiyar CAS, da ta kware a fannin kimiyyar kwayoyin halitta, gwaje-gwajen guda biyu, za su fayyace yanayin rayuwar kowace shuka a sararin samaniya da kuma gano yadda ake amfani da yanayin da ake kira microgravity, don shuka tsirran da kuma kara karfin samar da shuke-shuke a sararin samaniya. (Mai Fassarawa: Ibrahim Yaya)