Ana sa ran darajar kayayyakin da masana’antun kasar Sin ke sarrafawa za ta karu da fiye da yuan tiriliyan 8, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.13 a karkashin ci gaban kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14 na shekarar 2021 zuwa 2025, inda hakan zai ba da gudummawar fiye da kashi 30 bisa dari na ci gaban masana’antun duniya, kamar yadda wani jami’i ya bayyana a yau Talata.
Ministan masana’antu da fasahar sadarwa ta zamani Li Lecheng wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya kuma ce, kasar Sin ta ci gaba da rike matsayinta na zama babbar cibiyar masana’antu a duniya tsawon shekaru 15 a jere.
A cikin shekaru 5 da suka gabata, kasar Sin ta ci gaba da bunkasa zuba jarin kirkire-kirkire, tare da kakkafa manyan kamfanoni, wanda ko wannensu yana samun makudan kudin shiga na kasuwanci da ya kai akalla yuan miliyan 20 a duk shekara, kana suna kashe fiye da da kashi 1.6 na kudaden shigar da suke samu wajen gudanar da ayyukan bincike da samarwa (R&D).
Li ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta bi sahun kasashe da dama wajen kaddamar da shirin karfafa juriya da dorewar samar da kayayyakin masana’antu ba tare da tangarda ba, da nufin kiyaye hanyoyin samar da kayayyaki a duniya, da samar da karin hadin gwiwa, da kuma daidaito. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp