An gudanar da taron raya kasashen Afirka karo na 8 da kasar Japan ta jagoranta a kasar Tunusiya daga ranar 27 zuwa ta 28 ga wata.
Ko dai rahotannin kafofin yada labarai na kasar Japan ko kuma sauraron jawabai daban-daban da jami’an kasar Japan suka gabatar a yayin taron, wani abin da ake ji shi ne, a cikin alkawuran “taimakawa” Afirka da kasar Japan ta dauka, ana ganin yadda kasar Japan ta saka wasu abubuwan son kai nata a ciki, har ma ba zato kasar Sin ta zama wani jigon da kasar Japan ta kan ambata a yayin taro, ko da yake kasar Sin ba ta halarci taron ba.
A yayin taron, firaministan Japan Fumio Kishida ya sanar ta kafar bidiyo cewa, a cikin shekaru 3 masu zuwa, kasarsa za ta zuba jarin dalar biliyan 30 a kasashen Afirka, sannan za ta horas da kwararrun nahiyar dubu 300 da dai sauransu. Fumio Kishida ya jadadda cewa, “Wannan aiki ya sha bamban da na kasar Sin”. Jaridar Asahi Shinbunmafi, wato jarida mafi karbuwa a kasar Japan ta bayyana a cikin rahoton da ta wallafa a ranar 28 ga wata, cewar firaminista Fumio Kishida ya jaddada dangantakar dake tsakanin Japan da kasashen Afirka ne domin yana son rage tasirin kasar Sin a Afirka kawai.
A matsayinta na kasar da ta sha kaye a yakin duniya na biyu, ko da yake yanzu kasar Japan kasa ce mai arziki a duniya, amma ba ta son zama mai karfin tattalin arzki kawai, ta dade tana kokarin neman samun matsayi na siyasa a duniya. Zama wata mambar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, wata muhimmiyar hanya ce gare ta wajen cimma wannan buri.
A ’yan shekarun baya-bayan nan, a kullum kasar Japan ta yi amfani da manyan tarukan kasa da kasa iri iri, kamar taron raya kasashen Afirka, ta ce, yin gyare-gyare a kwamitin sulhu na MDD shi ne manufa ce daya ta Japan da kasashen Afirka.
A yayin taron na wannan karo, Japan ta sake gabatar da wannan ra’ayinta, kuma ta sake bayyana yunkurinta na daukar kasashen Afirka a matsayin “Gidan kuri’o’i” da kuma za ta gindaya sharuddan siyasa a lokacin da take samar da agaji. (Safiyah Ma)