Rundunar ‘yansandan Jihar Kano sun kama wasu maza uku da ake zargi da fashi a Abuja, tare da ƙwato wata motar sata.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Ismail Imran (20), Abdulaziz Yahaya (31), da Musa Ibrahim Isah (29).
- Amfani Da Karfin Tuwo Ba Zai Iya Kawo Zaman Lafiya A Yankin Gabas Ta Tsakiya Ba
- Shettima Ya Yaba Wa Uba Sani Kan Kafa Majalisar Ƙwarewa Ta Jihar Kaduna
An kama su ne ranar 6 ga watan Satumba, 2025, yayin wani samame.
An mayar da wata motar ƙirar Toyota Corolla mai launin shuɗi wadda aka lalata gilashinta na gaba.
An sace motar ne yayin fashin a yankin Durumi, a Abuja, ranar 5 ga watan Satumba.
‘Yan fashin sun raunata mutum ɗaya a cikin ‘yan gidan suka kai harin.
‘Yansanda sun ce an bi diddigin waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da tsauraran bincike.
‘Yansanda sun kuma yi gargaɗin cewa za su ci gaba da aiki tare da al’umma da ƙungiyoyi tdon hana aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp