Kasar Sin ta kasance kan gaba a duniya a yawan hakkokin mallakar fasaha, a masana’antun dake karkashin bangaren tattalin arziki na fasahohin zamani ko dijital a shekarar 2024, inda karuwar da ta samu ya zarce na matsakaicin adadin na duniya
A cewar hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta Sin, adadin hakkokin mallakar fasahar kirkire kirkire a wadannan masana’antu ya kai 500,000 a bara, adadin da ya karu da kaso 23.1 kan na mizanin shekara-shekara.
An fitar da wadannan alkaluma ne yayin taron shekara shekara kan hakkin mallakar fasaha na kasar Sin da aka yi wa taken “Hakkin Mallakar Fasaha a Zamanin Fasahohi da Na’urori.” (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp