An ɗauke gawar wani mutum da ba a kai ga tantancewa ba, wanda ya mutu sakamakon kamu da wayar lantarki ta yi masa a yayin da yake yunƙurin satar wata na’ura a (taransifoma) da ke cikin harabar Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri, babban birnin jihar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta nanata gargaɗi kan lalata kayan wutar lantarki a faɗin ƙasar.
- Wakilin VOA Haruna Dauda Ya Rasu A Maiduguri
- Bam Ya Hallaka Ma’aikatan Hukumar Ilimi 2 A Hanyar Damboa-Maiduguri
Jaridar PUNCH Metro ta rawaito a cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Ƴansanda na Jihar Borno, Kenneth Daso, ya fitar a ranar Lahadi cewa an gano gawar ne tun da sassafe.
A cewar Daso, binciken farko ya nuna cewa marigayin ya gamu da ajalinsa ne sakamakon riƙeƙar da wayar lantarki ta yi masa a yayin da yake ƙoƙarin lalata kayayyakin lantarki.
Ya ƙara da cewa ƴan sanda tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta jihar sun ɗauke gawar daga wurin, sannan suka fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
A cikin sanarwarsa, Daso ya ce: “Rundunar Ƴansanda ta Jihar Borno na sanar da jama’a cewa an gano gawar wani mutum da ba a tantance ba a kusa da na’urar sauya wuta (transformer) a Jami’ar Jihar Borno, Maiduguri.
“Binciken farko ya nuna cewa marigayin ya mutu ne sakamakon jan wutar lantarki yayin da yake ƙoƙarin cire kayayyakin lantarki.
“Rundunar ta fara cikakken bincike kan lamarin, kuma tare da haɗin gwiwar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Borno an kwashe gawar zuwa asibiti domin a gudanar da binciken likitanci yadda ya kamata.”
Ya jaddada cewa rundunar ta jajirce wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da yin gargaɗi ga mazauna jihar da su guji aikata lalata kayayyakin gwamnati.
Daso ya ƙara da cewa: “Kwamishinan Ƴansanda, Naziru Abdulmajid, ya sake gargaɗin dukkan masu aikata laifin lalata kayayyaki da su daina, domin hakan barazana ce ga rayukan mutane da kuma tsaron jama’a. Rundunar tana tabbatar wa da mutanen Jihar Borno cewa za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi tare da kira ga jama’a su kasance masu lura da kuma hanzarta kai rahoto kan duk wani motsi ko shakku a kusa da muhimman kayayyaki ga ofishin ƴan sanda mafi kusa.”
Sai dai duk da ƙoƙarin wayar da kan jama’a da gwamnatin tarayya ke yi game da illar lalata kayayyakin lantarki, ba a ga ƙarshen wannan matsala ba.
A watan Janairu, wani mutum da ba a san ko wane ba ya mutu a Akute, Jihar Ogun, bayan kamun lantarki a yayin ƙoƙarin lalata wata taransiforma. Kakakin Rundunar Ƴansanda ta Ogun, Omolola Odutola, ta ce mutumin ya hau cikin gidan na’urar, inda yake ƙoƙarin yanke wayoyi, sai lantarkin ya kashe shi.
Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (TCN) ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan haɗarin lalata kayayyakin wutar lantarki, musamman ga masu aikata hakan da kuma al’ummomin da abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp