Kungiyar likitocin Nijeriya (NARD), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi, kwanaki biyu bayan da mambobin kungiyar suka janye ayyukansu a asibitocin gwamnati a kasar.
Shugaban kungiyar, Dokta Tope Osundara, ya tabbatar da dakatarwar a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a daren ranar Asabar, inda ya umarci mambobin kungiyar da su koma bakin aiki a ranar Lahadi.
Ya ce matakin ya biyo bayan sauke nauyin wasu bukatu da gwamnatin tarayya ta yi wanda kungiyar ta gabatar wa gwamnatin tun a farko.
“An biya wasu bukatunmu, gwamnati ta yi alkawarin duba sauran bukatun, don haka, an dakatar da yajin aikin, za mu dawo wuraren ayyukanmu don ci gaba da aiki a ranar Lahadi, mun yi hakan ne domin nuna fatan alheri da kuma taimaka wa ‘yan Nijeriya da ke neman lafiya a cibiyoyinmu daban-daban,” in ji Osundara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp