Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya ce babu yiwuwar mulki ya koma Arewa a 2027, yana mai jaddada cewa Shugaba Bola Tinubu ya na da ikon kammala wa’adin shekaru takwas na mulkinsa.
Da yake magana a shirin Politics on Sunday na TVC, Bago ya bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na kamfen ɗin Tinubu na 2027, tare da bayyana cewa shalƙwatar yaƙin neman zaɓen za ta kasance a Minna.
- Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin RenewHER, Don Magance Mutuwar Mata
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Taya Gwamna Bago Murnar Cika Shekara 51
Ya ce tsarin karɓa-karɓa ya taimaka wajen tabbatar da daidaito a siyasar ƙasar, don haka duk masu neman dawo da mulki Arewa a yanzu ba su da gaskiya. Gwamnan ya ƙara da cewa matasa a yankin Arewa na goyon bayan Tinubu, kuma Jihar Neja za ta jagoranci tunkarar 2027.
Bago ya kuma kare manufofin gwamnatin Tinubu, inda ya ce cire tallafin man fetur ya ceci kuɗaɗen da ake karkatarwa zuwa amfani ƙashin kai, yanzu kuma ana amfani da su wajen ayyukan raya ƙasa. Ya ce gwamnatin Neja ma ta ninka kuɗaɗen shiga kuma tana aiwatar da manyan ayyuka ba tare da tangarɗa ba.
Gwamnan ya jaddada buƙatar kafa ƴansandan jihohi domin tabbatar da tsaro a yankuna, yana mai cewa: “Idan kowace ƙaramar hukuma ta ɗauki mutanenta, za a sauya labarin tsaro a Nijeriya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp