Ƴan bindiga sun kashe Sarkin Shuwaka na Garga, Mallam Hudu Barau, bayan da suka yi garkuwa da shi a ƙaramar hukumar Kanam, Jihar Filato.
Ƙungiyar cigaban Kanam (KADA) ce ta tabbatar da lamarin a wata sanarwa da shugabanta, Shehu Kanam, da sakatare, Barr. Garba Aliyu, suka fitar a ranar Litinin.
Sun bayyana cewa an yi garkuwa da Sarkin ne kwanaki shida da suka gabata, daga bisani aka kashe shi, inda aka gano gawarsa a dajin Wanka.
- Sojoji Sun Kama Ɗan Bindiga Ɗauke Da Makamai A Jihar Filato
- Filato Ta Tsakiya Ta Amince Da Tazarcen Mutfwang A 2027
KADA ta yi kira da a gaggauta ɗaukar matakin tsaro, tana mai cewa mutanen Garga da kewaye na rayuwa cikin tsananin fargaba saboda hare-haren ƴan bindiga da ke ci gaba da kashe bayin Allah da yin garkuwa da su. Sun zargi gwamnati a matakai daban-daban da rashin ɗaukar matakan da suka dace don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ƙungiyar ta bukaci Gwamna Caleb Mutfwang ya ayyana dokar ta baci a Garga tare da tura jami’an tsaro cikin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar. Haka kuma, sun caccaki ƴan majalisar tarayya da na jiha na yankin da cewa ba sa taka rawar da ta dace wajen kawo ƙarshen hare-haren da ke addabar al’umma.
KADA ta yi gargaɗi cewa haƙurin jama’a ya ƙare, tana mai jaddada cewa shiru da halin ko-in-kula daga shugabanni ba za a ƙara yarda da shi ba. Sun yi kira da a tabbatar da adalci da kuma mayar da zaman lafiya a yankin, tare da nuna goyon baya ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Garga.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp