An yi garkuwa da wani malamin krista na ɗarkar Katolika dake Agaliga-Efabo, a ƙaramar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi, Rev. Fr. Wilfred Ezemba, ta amfani da bindiga. Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 13 ga Satumba, 2025, a Imane, inda aka rawaito cewa an kuma sace wasu fasinjoji tare da shi a hanyar Imane-Ogugu Road.
Wannan lamari ya jefa mabiya cocin Katolika a cikin tashin hankali domin zuwa yanzu masu garkuwar ba su tuntuɓi kowa daga cikin iyali ko mambobin cocin ba. Wani Malamin Coci a yankin, Fr. Michael, ya bayyana cewa suna cikin ruɗani, amma suna da ƙwarin gwuiwar cewa addu’o’insu za su taimaka wajen kuɓutar da abokin aikinsu.
Jami’an tsaro sun fara aikin bincike da ceto, inda rundunar ƴansanda, da sojoji da ƴan sa kai daga Kogi East Neighbourhood Watch (KENW) suka shiga daji suna bin sawun masu garkuwar. Wannan na zuwa ne mako guda bayan wani lauya, Barr. A. B. Shaibu, ya shiga hannun masu garkuwa a yankin kuma aka sako shi bayan iyalinsa sun biya kuɗin fansa.
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Fasto Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani ɗan cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya ƙara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi ta gabas.