Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya shaidawa gwamnonin jihohi da ‘ya’yan jam’iyyarsa ta APC cewa, gwamnatinsa ba za ta tsoma baki ba a zaben 2023.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya fitar da sanarwar jim kadan bayan tattaunawar da Gwamnonin jam’iyyar APCn sukayi da Shugaba Buhari a wata ziyara da suka kaimasa a fadar gwamnati dake Abuja a ranar Talata.
A cewar Adesina, Buhari ya shaida wa gwamnonin cewa rashin tsoma baki a zabe yana tabbatar da tsarin siyasa, yana tabbatar da Gaskiya da adalci da nutsuwa acikin masu zabe, sannan kuma ya nuna cewa jam’iyya mai mulki na mutunta masu zabe.
Shugaban ya ce zaben gwamnoni da aka gudanar a Anambra da Ekiti da kuma Osun ya burge shi, inda ya ce bai tsoma baki ba.
APC ta sha kaye a zaben gwamna a Anambra da Osun amma ta samu nasara a Ekiti.
“Ina so ’yan Nijeriya su sani cewa muna girmama su, kuma za mu ba su damar zaben wanda suke so.” Inji Buhari.