Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta maka tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, tare da kafafen sada zumunta Facebook da X a kotu.
Ƙarar mai ɗauke da tuhuma biyar an shigar da ita ne gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
- Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
- Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana
Wannan ya biyo bayan ƙin cire wasu rubuce-rubuce da Sowore ya wallafa a kan Shugaba Bola Tinubu.
Lauyoyi daga Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da kuma na DSS ne suka shigar da ƙarar.
Tun da farko, DSS ta aike wa X takarda kan neman a rufe shafin Sowore.
Ta kuma ba shi umarnin ya goge rubutun da ta ce ya ci zarafin shugaban ƙasa.
Sai dai Sowore ya ƙi sauke rubutun da ya wallafa.
Ya rubuta a shafinsa na X cewa: “DSS ta shigar da ƙara mai tuhuma biyar a Babbar Kotun Tarayya a Abuja a kaina, X da kuma Facebook.
“Sun ce wai na aikata wasu sabbin laifuka saboda na kira Tinubu ‘ɓarawo’. Duk da haka, zan halarci kotu duk lokacin da aka fara shari’ar.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp