Hukumar kula da ikon mallakar fasahohi ta duniya WIPO, ta ce a shekarar nan ta 2025, kasar Sin ta daga zuwa mataki na 10, a jadawalin kasashen dake kan gaba a fannin kirkire-kirkire, inda ta kara mataki guda kan na shekarar da ta gabata, kuma a karon farko ta shiga jerin kasashe 10 na farko a jadawalin.
A yau Talata ne WIPO ta fitar da rahoto mai kunshe da jadawalin na GII na 2025, wanda ya fayyace kwazon kasashe da yankunan duniya kusan 140 a fannin kirkire-kirkire, ta amfani da mizani daban daban har kimanin 80, wadanda suka hada da yawan kudaden da ake shigarwa a bangaren bincike da samar da ci gaba, da kudaden jari da ake zubawa a fannoni masu yiwuwar gamuwa da asara, da fitar da hajojin manyan fasahohi, da neman rajistar kariyar mallakar fasaha.
Rahoton ya kuma bayyana yadda kasar Sin ke wanzar da jagoranci tsakanin kasashe masu matsakaicin kudin shiga, da ci gaban da take samu a fannin zuba jari a bangaren bincike da samar da ci gaba, da fitar da hajojin manyan fasahohi, da kayayyaki dake zama sakamakon kirkire-kirkire.
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp