Mataimakin shugaban jam’iyyar APC, na Jihar Nasarawa, Hon. Aliyu Yakubu Barde, ya rasu.
Iyalan marigayin sun ce ya rasu ne a ranar Talata a Lafia bayan gajeriyar rashin lafiya.
- Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
- Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
Za a yi jana’izarsa a garinsu Wamba bisa tanadin addinin Musulunci.
Rasuwarsa ta jefa jam’iyyar mai mulki a Jihar cikin jimami.
Sakataren jam’iyyar APC na jihar, Cif Otaru Douglas, ya tabbatar da rasuwar tare da bayyana hakan a matsayin babban rashi ga jam’iyyar da jihar baki ɗaya.
Kafin ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Barde ya taɓa zama Shugaban riƙo na Karamar Hukumar Wamba a zamanin tsohon Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp