Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce kasarsa na goyon bayan shawarar da Sin ta gabatar ta tsarin shugabancin duniya, kuma ta shirya ba da gudummawa wajen inganta tsari mai adalci da inganci.
Embalo ya bayyana haka ne jiya, lokacin da yake yaba wa ci gaban dangantakar kasashen biyu, yayin ganawa da jakadan Sin a Guinea-Bissau Yang Renhuo. Ya kara da cewa, Guinea-Bissau tana fatan ci gaba da kara zurfafa hadin gwiwa da Sin a fannoni daban-daban, da kuma inganta ma’anar dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare, tare da ba da gudummawa wajen inganta tsarin shugabancin duniya mai adalci da inganci.
A nasa bangare, jakada Yang ya bayyana cewa, shawarar ta dace da yanayin tarihi, kuma tana da ma’ana a bangaren kimiyya da ba da jagoranci ga mabambantan ayyuka, wadda kuma ke nuna alhakin dake wuyan kasar Sin. Har ila yau, ya ce Sin tana fatan hadin gwiwa da kasashe masu tasowa, ciki har da Guinea-Bissau, don tabbatar da aiwatar da shawarar, tare da kafa kyakkyawar makomar bil adam ta bai daya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp