• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

by Rabi'u Ali Indabawa
2 months ago
Farashin

Mashawarci na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tattalin Arziki, Tope Fasua, ya bayyana
cewa Ƴan Nijeriya za su iya sa ran hauhawar farashi zai sauka zuwa kashi ɗaya cikin ɗari nan ba da
jimawa ba, abin da ya yi imani zai sauƙaƙa rayuwar al’umma.
Fasua ya bayar da wannan tabbaci ne a lokacin da ya bayyana a shirin The Morning Brief na Channels Teleɓision a ranar Talata. Ya yi bayanin cewa farashin abinci yana fara raguwa yayin da hauhawar farashi ke ƙara saukowa.

Bayanan nasa sun biyo bayan rahoton Hukumar Ƙididdiga (NBS) wanda ya nuna cewa hauhawar
farashin kayayyaki ta kai kashi 20.12 a watan Agusta 2025, daga 21.88 a watan Yuli.
A cewar NBS, hauhawar farashin kayayyaki na watan Agusta 2025 ya nuna raguwar kashi 1.76 idan aka
kwatanta da watan Yuli. A kowane wata, hauhawar farashi ta kan kai kashi 0.74, yayin da a watan Agusta, hauhawar farashin abinci ya kasance kashi 1.65.

A shekara-shekara, hauhawar farashi yana raguwa da kashi 12.03 idan aka kwatanta da kashi 32.15 da aka
samu a watan Agusta 2024.

  • DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur
  • Tinubu Ya Bayar Da Umarni Karya Farashin Kayan Abinci A Nijeriya

Hukumar ƙididdiga ta bayyana cewa duk da hauhawar farashin na nan, saurin ƙaruwar farashin kayayyaki
yana raguwa idan aka kwatanta da watannin da suka gabata. Dangane da iƙirarin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, cewa Ƴan Nijeriya na “mutuwa da yunwa kullum,” Fasua ya ce:
“Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kawai ya sanya siyasa ce cikin lamarin a
ƙoƙarinsa na son ya samu shiga ofishin shugaban ƙasa, ni kuma ba na yin tsokaci a harkokin siyasa.

“Ba lallai bane ya yaba da nasarorin gwamnatin yanzu ba, amma dai ya kyautu mu tsaya kan gaskiya da
tabbatattun bayanai.”Fasua ya amince cewa kashi 20.12 har yanzu babban kaso ne, amma ya jaddada cewa waɗannan lambobin yanzu sun nuna sabuwar ƙididdigar da aka daɗe ana jira. Ya bayyana cewa: “Hauhawar farashi na kashi 20.12 har yanzu mai girma ne a wasu fannonin tattalin
arziki saboda abin da yake nufi shi ne farashin kayayyaki na ci gaba da hauhawa a wasu fannoni, amma
ba kamar yadda aka saba ba.

LABARAI MASU NASABA

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su. “An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na son zuciya da wani ke ganin ya kamata mu kasance kusa da kashi 30, wannan ra’ayinsu ne kawai. Muhimmin abu shi ne an sabunta ƙididdiga watanni da dama da suka wuce, kuma abin da muke gani yanzu shi ne raguwar hauhawar farashi da ta ci gaba.” Fasua ya kuma ambaci cewa Naira ta samu tagomashi a kwanakin baya kuma farashin mai na hauhawa a kasuwar duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 
Manyan Labarai

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya
Manyan Labarai

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro
Manyan Labarai

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Next Post
Farashin

2027: Su Wane Ne Ke Tsoron Guguwar Makinde A Jam’iyyar  PDP

LABARAI MASU NASABA

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.