• English
  • Business News
Saturday, September 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

2027: Su Wane Ne Ke Tsoron Guguwar Makinde A Jam’iyyar  PDP

by Bello Hamza
18 hours ago
in Labarai
0
Makinde
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Lokacin da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa karo na 102 ta yanke shawarar ware takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027 ga Kudu, yanayin siyasa a ƙasar ya ɗauki zafi tare da ɗimbin ce-ce-ku-ce kan wane ne zai ɗauki tikitin babbar jam’iyyar adawa a Afirka.

Masu sharhi kan siyasa da wasu masu adawa, musamman daga jam’iyyar mai mulki ta APC, tun da farko sun yi gaggawar cewa PDP ta mutu kuma ta shirya zuwa maƙabarta. Sai dai abin mamaki, jam’iyyar da ake ganin ta mutu ta sake tashi, inda ta ayyana watan Nuwamba a matsayin lokacin da za ta gudanar da babban taron zaɓen shugabanni a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

  • Ɗan Majalisa Zai Saya Wa Makinde Fam Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa A 2027
  • Makinde Ya Amince Da N80,000 A Matsayin Mafi Karancin Albashin Ma’aikata

Zaɓen Ibadan a matsayin wurin gudanar da babban taron PDP ya haifar da fargaba musamman a cikin sansanin jam’iyya mai mulki, game da abin da ka iya kasancewa sakamakon babban zaɓen 2027 idan PDP ta tsara komai yadda ya kamata.

Wannan fargaba ba ta tsaya ga jam’iyyar APC kaɗai ba, har ma da wasu manyan jiga-jigai a cikin PDP da suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu na APC abin da da dama suka kira babbar hujja ta korarsu daga jam’iyyar, yanzu sun fara jin tsoron sabuwar PDP da ke tasowa.

Wasu masu nazarin siyasar Nijeriya sun bayyana ayyukan cin amanar jam’iyya da ke gudana a PDP a matsayin abin da bai taɓa faruwa ba tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999. Amma yayin da PDP ke ƙoƙarin sake farfaɗowa don shirye-shiryen manyan zaɓuka masu zuwa, sabon yanayin da ya kunno kai ya sa aka fara tambayar nan mai muhimmanci. Wanene ke tsoron Seyi Makinde, Gwamnan Jihar Oyo?

Labarai Masu Nasaba

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Idan aka yi ɗan nazari kan tafiyar siyasar Seyi Makinde a Jihar Oyo da kuma yammacin Nijeriya gaba ɗaya, za a fahimci sosai wane ne Makinde da kuma dalilin da ya sa ya dace kowanne ɗan siyasa mai hangen nesa ya yi hattara da shi kafin 2027.

Ko da yake Gwamnan Jihar Oyo, wanda ake kira da “Star Boy”, ya kafa kansa a matsayin jagoran PDP a yankin yamma, tafiyarsa zuwa kujerar gwamna ba ta zo masa da sauƙi ba.

Kafin shekarar 2019, Makinde ya tsaya takarar kujerar Sanatan Oyo ta Kudu a shekarar 2007, amma ya sha kaye a hannun Kamoru Adedibu. Duk da wannan rashin nasara ta farko, bai karaya ba. A 2010, ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya sake neman kujerar Sanata na Oyo ta Kudu a zaɓen 2011, amma ya sha kaye a zaɓen fid da gwani a hannun sanatan da ke riƙe da kujerar a lokacin.

A 2014, Makinde ya nemi tikitin PDP domin takarar gwamnan Jihar Oyo a zaɓen 2015. Amma a watan Disamba 2014, bayan kammala zaɓen fid da gwani, jam’iyyar ta hana shi samun tikitin gwamna. Duk da haka, Makinde ya ci gaba da jajircewa bisa burinsa na yi wa al’ummar Oyo hidima, yana mai dagewa kan hangen nesansa na ci gaban jihar.

A ranar 29 ga Satumba 2018, Makinde ya zama ɗan takarar gwamna na PDP a babban zaɓen 2019 a Jihar Oyo, bayan ya samu ƙuri’u 2,772 a zaɓen fid da gwani. Kamar yadda ya bayyana a lokacin: “Mutanen Oyo ne suka yanke shawara a 2019. Ba mu da wani uba a siyasa. Babu wanda ya ɗauki nauyinmu. Babu wanda ya ba mu ko sisin kobo don mu kai ga nasara.”

Yau, Makinde ya shafe sama da shekaru shida daga cikin shekaru takwas da kundin tsarin mulki ya amince masa ya yi a matsayin Gwamnan Jihar Oyo. Ko da yake bai bayyana niyyarsa game da 2027 ba tukuna, tursasawa da kira gare shi da ya shiga fagen takarar na ƙara ƙarfi a kullum.

Masu nazarin siyasa na ci gaba da sa ido kan matakan da zai ɗauka a nan gaba yayin da wa’adin gwamnatinsa na biyu ke gab da ƙarewa. Wata makoma ce da dama a cikin jam’iyyar mai mulki, da ma wasu daga cikin PDP, ke ganin abin tsoro ne da damuwa.

A 2019, Makinde bai dogara da wani uban gidan siyasa ba, amma ya samu nasarar zama gwamnan Jihar Oyo. A yau kuma, mutane da dama a faɗin ƙasar na ganin cewa, idan ya yanke shawarar tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, akwai yiwuwar ya maimaita irin “sihirin nasara” da ya yi a Oyo.

Da yawa na ganin cewa dama tana gefensa daga zaɓen fid da gwani na PDP har zuwa babban zaɓen shugaban ƙasa a 2027. Ko da yake bai fito fili ya sanar da niyyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa ba tukunna, amma shahararsa da ke ƙara bunƙasa a cikin PDP da wajenta, na nuna irin ƙarɓuwar da yake samu a matakin ƙasa, wanda ya sa ake kallonsa a matsayin babban ƙalubale ga duk wani ɗan takarar APC a gaba.

Gwamna Makinde, saɓanin wasu a cikin jam’iyya, ya tsaya tsayin daka kan aƙidar PDP, ya tsaya tare da jam’iyyar a lokutan ƙalubale.

A lokacin da manyan jiga-jigan PDP suka gudu suka koma APC da sunan neman haɗuwa da “cibiya mai ƙarfi”, Makinde bai bar jam’iyyar ba, maimakon haka ya tallafa mata da dukiya da albarkatu.

A yau, farin jinin Gwamna Seyi Makinde ya kai kololuwa, yana ratsawa cikin dukkanin shiyyoyin ƙasar shida. Wannan ya sanya jam’iyyar mai mulki cikin fargaba, yayin da salon jagorancinsa ke ƙara yin ƙarfi har zuwa wajen nahiyar Afirka.

An gwada farin jinin Gwamna Makinde a ranar 16 ga Agusta, 2025, lokacin da aka gudanar da zaɓen cike gurbi na majalisar tarayya a Ibadan North Federal Constituency. Ɗan takarar PDP, Fola Oyekunle, ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu ƙuri’u 18,404, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na APC, Adewale Olatunji, wanda ya samu ƙuri’u 8,312.

An gudanar da wannan zaɓe ne domin cike gurbin rasuwar Hon. Olaide Akinremi ta bari.

Sakamakon ya nuna nasara mai ƙarfi ga PDP a Jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Makinde, tare da zama shaida kan tasirinsa da kuma gagarumin farin jininsa a jihar, abin da ke sa abokan hamayyarsa a fagen siyasa cikin fargaba.

A ƴ an kwanakin nan ma, wata ƙungiyar masu goyon bayan PDP mai suna Reset Lagos PDP ta yi kira ga al’ummar Inyamurai (Igbos) a faɗin ƙasar da su haɗa kai wajen mara wa Gwamna Makinde baya domin ya karɓi mulki a shekarar 2027.

Mai shirya ƙungiyar, Dr Adetokunbo Pearse, wanda shi ma shugaban National Support Group for Makinde ne, ya shaida wa manema labarai cewa Makinde ya bambanta da sauran masu sha’awar takara, kuma yana da gaskiya da sha’awar ci gaban al’ummar Igbo a zuciyarsa.

Ya ce, “Shi ne kaɗai ya nuna sha’awa a tsayawa takara, kuma ya yi bajinta sosai a matsayin gwamnan Jihar Oyo. Ya shiga siyasa ba tare da dogaro da kuɗin gwamnati ba, tun daga jami’a, saɓanin yawancin ƴ an siyasa da ke shigowa da komai a hannunsu sannan su fara dogaro da dukiyar gwamnati.”

A gefe guda, shugaban reshen Legas na Igbonine Great Peoples Assembly, Elder Okezie Anyanwu, ya bayyana cewa zaɓen 2027 ba zai kasance yadda aka saba ba, inda ya yi kira ga Inyamurai da ke Legas da su haɗa kai da PDP, wacce ya bayyana a matsayin jam’iyya mai ingantattun tsare-tsare a Legas.

Ya ce, “Dalilin da ya sa na ke tare da PDP shi ne ita ce kawai jam’iyya da ke da tsari a kowane sashi na Nijeriya. Kuma tubalin PDP ya ta’allaƙa ne kan nagarta da gaskiya saɓanin waɗannan jam’iyyun da suka fito daga baya. Ina kira ga kowa da kowa da ya kada ƙuri’a yadda ya dace.”

Idan za a iya tunawa wata ƙungiya mai suna ‘Nigeria Youths Awareness Group Makinde 2027’  (NYAG Makinde 2027), a watan Mayu, yayin taron manema labarai a Kano kan hasashen siyasar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ta bayyana a fili cewa tana alfahari da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin mutumin da zai iya ciyar da Nijeriya gaba.

Ƙungiyar ta bayyana cewa dukkanin ƴ an Nijeriya masu kishin dimokuraɗiyya ya kamata su haɗa kai a bayan Makinde ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba, domin tabbatar da samun tikitin tsayawa takara.

Yayin ganawa da manema labarai a Kano, Alhaji Lawal Abdullahi, Sakataren Ƙasa na ƙungiyar, ya bayyana cewa: “Mun haɗu a matsayin ƙungiyoyi daban-daban kuma mun amince mu yi tafiya tare domin Seyi Makinde ya zama shugaban ƙasa a 2027. Mu jirgin da ke tafiya ne, babu wani abu da zai iya tsayar da mu sai mun cimma burinmu na shugabancin Seyi Makinde.”

Gwamna Seyi Makinde tun da farko ya kasance mai jituwa da Arewacin ƙasar nan a harkokinsa na siyasa, tattalin arziƙi da kuma zamantakewa. A lokacin da rikicin jam’iyyar PDP ya yi tsanani, Makinde a tattaunawarsa da manyan jiga-jigan jam’iyyar daga Arewa ya taka rawar gani wajen sasanta al’amura domin kuɓutar da PDP daga rugujewa.

Makinde bai taɓa ɓoye matsayinsa kan batutuwan jam’iyya ba. Yayin hira da ƴ an jarida kwanan nan bayan taron tunawa da cikar shekara 10 da naɗin Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi, ya yi tsokaci kan ficewar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, daga PDP. Ya ce: “Siyasa wasa ne na muradu.

Ban yi imani cewa ficewarsa zai bar wani giɓi ga PDP a matsayin jam’iyya ba. PDP wata ƙungiya ce mai ƙarfi. Muna da ƴ ancin shiga da fita. Duk wanda yake riƙe PDP da hannunsa, gara ya fice.

Abin da ya kamata mu fahimta shi ne: ƴ an wasa suna zuwa suna tafiya, gwamnoni suna zuwa suna tafiya, shugabanni suna zuwa suna tafiya, amma jiharmu da ƙasarmu za su ci gaba da wanzuwa.”

A nasa ɓangaren, Hon. Dare Adeleke, wanda shi ne mai ba wa Gwamna Makinde shawara kan harkokin Mazaɓu na Tarayya, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki APC na cikin firgici da tasirin Makinde a siyasar ƙasar kafin 2027.

Adeleke ya ce: “APC na cikin tsananin tsoro da yiwuwar tikitin Makinde a ƙarƙashin PDP. Sun san cewa idan ya tsaya takara, hakan na iya zama mummunan hasashe ga mulkinsu mai cike da gazawa, mulki da ake iya cewa shi ne mafi ban takaici a tarihin Nijeriya.”

Shaharar Makinde a faɗin ƙasar ta zama babban ƙalubale ga waɗanda ya doke sau biyu a Jihar Oyo. Suna fargabar cewa zai maimaita irin wannan nasara idan ya shiga fafatawar shugaban ƙasa a 2027.

Ga jiga-jigan PDP da ke da wannan ra’ayi, Gwamna Makinde na da ƙwarewa da cancantar da za su iya kai jam’iyyar ga nasara a babban zaɓen 2027.

Yayin da tafiyar 2027 ke ƙara bayyana a fili, ƴ an Nijeriya na jiran ganin fitattun ƴ an siyasa sun fito da kundin ayyukansu da zai nuna irin mulkin da suka yi da kuma abin da za su iya kawowa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban

Next Post

GORON JUMA’A 19-09-2025

Related

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta
Labarai

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

5 hours ago
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?
Manyan Labarai

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

8 hours ago
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

9 hours ago
Makinde
Labarai

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

10 hours ago
An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki
Labarai

An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki

12 hours ago
Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi
Labarai

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

12 hours ago
Next Post
GORON JUMA’A 01-07-2025

GORON JUMA'A 19-09-2025

LABARAI MASU NASABA

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

September 19, 2025
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

September 19, 2025
An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

September 19, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

September 19, 2025
Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

September 19, 2025
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

September 19, 2025
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

September 19, 2025
Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

September 19, 2025
Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

September 19, 2025
Makinde

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

September 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.