• English
  • Business News
Saturday, September 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Murnar Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (2)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
13 hours ago
in Labarai
0
Manzon
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ƴan’uwa masu bibiyarmu a wannan shafi assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barkatuh. A yau ma za mu ci gaba da wannan darasi na murnar cikar Haihuwar Manzon Allah (SAW) shekara 1500 a duniya. Saboda ƙara fahimtar darasin yau, za mu yi matashiya da ƙarshen karatun da ya gabata. 

Annabi Isah (AS) ya zo da abubuwa masu sauƙi, ya yada littafan da suka zo kafin sa, Allah ya sanya sauƙi a cikin lamarinsa, Allah ya sanya sauƙi a cikin mutanensa, don haka Ƴan Adam suka karɓa, amma saboda sauƙi (domin duk abu in ya yi sauƙi to ya zama na Ƴan Adam baki ɗaya, haka kuma duk abu in ya yi tsauri to iya naku ne). Daga nan har Allah ya kawo Bulus, wanda almajirin Annabi Isah ɗin ne, shi kuwa Bulus gaba ɗaya ma sai ya watsar da dokokin Attaurar ma, sai ya ɗauki “wasayal ashri” ɗin nan, kawai abin da ya ɗauka a cikin Attaura kenan. To mu ma ikon Allah, wannan “wasaya” guda goma Allah ya tafi da su a cikin Ƙur’aninmu, ita ce “Furƙánu”.

  • Nan Ba Da Jimawa Ba Hauhawar Farashin Kayayyaki Za Ta Zama Tarihi —Fadar Shugaban
  • Muna Murna Da Maulidin Cikar Manzon Allah (SAW) Shekara 1,500 Da Haihuwa (1)

To, amma idan muka zo wajen Annabi Muhammad (SAW) wanda shi ne ƙarshen ma’aika, shi kuwa Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya tattaro karatun fasahar “Engineering” ɗin gaba ɗaya ya damƙa masa (SAW). Duk littafin tafsirin da ka duba za ka ga ana yin sa ne daidai da wayewar al’ummar lokacin amma Alƙur’anin kansa na farko ne na ƙarshe ne, wata fahimtar ma tasa ba ta zo ba sai nan gaba.

To Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam a wajen kira shine ƙarshe a cikin Annabawa, yanzu duk haram Allah ya tattare masa ita, gata nan a cikin Al-ƙur’ani mai girma, mun yi bayani a karatun tafsirinmu na bana ga su nan wajen guda 28 ko guda 38. Sauran kuwa, Malamai sun kafa wata ƙa’ida; a kula da wannan ƙa’ida duk da dai ba a amfani da ita, sun ce “komai halak ne sai abin da Shari’a ta haramta”, to a Kur’ani za ka ga duk abin da Allah ya haramta za ka ga ya ce masa “hurrimat…”, ayoyi goma sha huɗu (14) suka zo da “hurrimat” amma kuma abubuwan da aka haramtawa a ciki wajen guda talatin da takwas (38) ne! To saura kuwa duk halal ne. 

Amma halal ɗin ma ai ba ko wanne za ka iya ci ba, akwai halal ɗin da bai dace da kai a ɗanɗanonka ba, ko bai dace da ɗabi’arka ba duk da halal ne, amma kai wani da ka gan shi ma sai ka yi amai! Akwai halal ɗin da bai dace da yanayin al’adar al’ummarka ba, ko wacce ƙabila za ka ga suna da wani abu wanda a ƙa’idarsu ba sa amfani da shi, duk da da cewa ba Allah ne ya haramta masu ba. To ba laifi, ku zauna a haka, amma kuma kar ku ce dole kowa sai ya zama haka. Ka ga akwai wani lokaci da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam aka kawo abinci da nama a ciki sai bai ci naman ba, aka tambaye shi “haram ne?”

Labarai Masu Nasaba

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Sai yace “A’a ba haram ba ne, kawai dai mutanena ba su san shi ba ne.” Annabi (SAW) ya taɓa cewa kar a ci tafarnuwa a shigo masallaci, aka tambaye shi: “Ya Rasulallah haram ne?” Sai ya ce “A’a ba na haramta abin da Allah bai haramta ba, kawai dai ni ne ba na son shi”, ka ga bambancin ladabin malamai na wancan zamani da na yanzu, a yanzu duk abin da wani Malami ba ya so sai kawai ya haramta shi. Amma duk inda Allah ya ce “hurrimat…” To wannan na Azal da Abadan ne. Kuma dokokin ko wace ƙasa za ka ga duk abubuwan da Allah ya haramta a Alƙur’ani ɗin nan guda 38 su ma sun haramta shi a dokar ƙasarsu. To yanzu kuma halal ɗin nan, Allah ya yarda idan wani hali ya zo to hukumar majalisar dokoki za ta iya hanawa, ƙabila za ta iya hanawa, kai ma za ka iya hana kanka!

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ma’aikin Allah ne, Annabin Allah ne, sannan kuma shugaban ƙasa ne a wancan lokacin, shi yake tsara dokokin ƙasa (constitution) na ƙasarsa (Sallallahu Alaihi Wasallam), don haka yana hana wasu abubuwan kuma ya halatta wasu abubuwan, kamar yanda aka taɓa tambayar Abdullahi ɗan Abbas, sai ya ce: “to wallahi ni ma doka kaza da kaza ban sani ba na wucingadi ne ko kuwa na dindindin ne”. Don haka, majalisar dokoki ba za ta ce “na haramta kaza” ba, sai dai ta ce “na hana kaza saboda dalili kaza”, to duk ranar da wannan dalilin ya ɗauke sai ka ji an janye wannan hanin kuma.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shari’arsa ta zo a mai tafiya ce, shi cikamakon Ma’aika ne, cikamakon Annabawa ne, don haka komai nasa na har ƙarshen halitta ne, don haka ne ya zamo rahama ga halitta gaba ɗaya. Don haka babu wanda za ka je masa da faɗa ka tilasta masa ya karɓi ra’ayinka, Manzo ne, Ma’aiki ne ga duk duniya gaba ɗaya, ya zo ya daidaita addininsa a cikinmu, ya yaɗa zaman lafiya a cikinmu, ya yaɗa girmama ɗan Adam; dama abu biyu ne addini; Allah ya saka ma Shehu Ibrahim (RTA) da alheri, yana cewa: “abu biyu ne addini, Girmama Allah da tausayin ɗan Adam, wannan shine addini”, duk abin da za ka ga addini yana kira, za ka ga a kan waɗannan abubuwan biyun ne. Don haka suka ce: “duk addinin da ya kira ka zuwa cewa  kar ka tausaya ma ɗan Adam to ba daga Allah yake ba”. Domin Allah shi ya halicci ɗan Adam ɗin nan, shi ya busa masa ransa, to kuwa Allah Tabaraka wa Ta’ala ba zai wulaƙanta ɗan Adam ɗin nan ba. 

Mutum kansa idan ya ƙera tukwane, ba zai yadda haka kawai wani ya zo ya farfasa masa tukwanensa ba, haka idan ka sayi sabon abin hawa ba zaka yarda kawai wani ya zo ya farfasa maka shi ba, da yara sun zo suna wasan jifa a kusa da abin hawan ka zaka kore su ne, ba don kar su fasa maka kai ba ne, a’a, domin kar su fasa maka abin hawan nan naka, to ka ga ta yaya Allah shi kuwa zai bar halittarsa a zo ana aibata ta ana halaka ta? Wallahi mu ji tsoron Allah. Wannan ya jawo ake mayar da addininmu baya. Manzon Allah ya zo ya yaɗa zaman lafiya, ya yaɗa girmama ɗan Adam, ya yaɗa soyayya a tsakaninsu, ya yaɗa daidaito a tsakanin ƙabilu da jinsunan mu, ayar Alƙur’ani ta ce, “Ya ayyuhan nasu innaa khalaƙnakum min zakarin wa untha, wa ja’alnaakum shu’uban wa ƙaba’ila lita’arafu; inna akramakum indallahi atƙaakum”. Ma’anar wannan aya ta sama tana nufin ko da Bayahude ko Bamajuse ko kuma ɗan kowanne addini idan ya fi ka tsoron Allah, to fa ya fika a wajen Allah, domin Allah “ya ayyuhan nasu” ya ce ba “ya ayyuhal muslimuna” ba. 

Akwai wani Bature, ya karanta littafan Annabawa da suka gabata da duk sauran littafan da ake cewa Allah ne ya saukar dasu, ya dudduba ya yi nazari, sai da Allah ya kawo shi Misra, ya haɗu da abokinsa sai ya sami ganin Kur’ani ta wajen abokin nan nasa kuma abokin ya tabbatar masa cewa shi ma wannan littafi daga Allah ne, sai ya ce to a ba shi ya duba (watau Alkur’ani mai fassara zuwa Ingilishi). Yana fara karantawa sai kuwa ya ce: “Haba! Yanzu na ji Allah ne yake magana! Amma duk waɗancan sauran littafan ina jin wani mutum ne abokina ko wani sarki mutum ne yake magana!”


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Maulud 1,500: Yadda Zawiyar Ahlul Faidhati Mai Diwani Group Ta Yi Maulidin Takutaha A Kaduna 

Next Post

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

Related

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta
Labarai

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

3 hours ago
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?
Manyan Labarai

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

6 hours ago
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

7 hours ago
Manzon
Labarai

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

8 hours ago
An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki
Labarai

An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki

10 hours ago
Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi
Labarai

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

10 hours ago
Next Post
Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

Wata Mata Ta Ƙona Al’aurar Ƙaramar Yarinya A Bauchi

LABARAI MASU NASABA

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu

September 19, 2025
Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

Yadda Ciwon Hanta Ke Yaɗuwa Tsakanin Ma’aurauta

September 19, 2025
An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

An Kammala Taron Dandalin Tattauna Batun Tsaro Na Xiangshan

September 19, 2025
Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

Firaministan Sin Zai Halarci Babban Taron Mahawara Na MDD Karo Na 80

September 19, 2025
Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

Shugaba Xi ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka

September 19, 2025
Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

Dokar Hana Ƙara Kuɗin Makaranta A Kaduna: Alheri Ce Ko Barazana Ga Makarantu Masu Zaman Kansu?

September 19, 2025
Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

Tinubu Ya Ziyarci Iyalan Buhari A Jihar Kaduna

September 19, 2025
Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata

September 19, 2025
Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

Ofishin Yada Labarai Na Majalisar Gudanarwar Kasar Sin Ya Fitar Da Takardar Bayani Mai Taken “Nasarar Aiwatar Da Manufar JKS A Xinjiang A Sabon Zamani”

September 19, 2025
Manzon

Tarihin Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa

September 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.