Ƙaramar Hukumar Faskari a jihar Katsina ta bi sahun sauran ƙananan hukumomi wajen shirya taron zaman sulhu da ɓarayin daji domin samun zaman lafiya a wannan yanki.
Ita dai ƙaramar hukumar Faskari ita ce ta takwas da ta shiga wannan yarjejeniyar zaman lafiya da ɓarayin daji gwamnatin jihar Katsina ke cewa ba ruwan ta, amma dai zata dauki mataki akan duk wanda ya karya Yarjejeniyar.
Wannan zaman sulhu ya ɗauki hankali fiye da kowane musamman ganin wasu fuskokin manyan ɓarayin daji da suka halarci taron wanda masana ke cewa lallai a sanya hankali da tunani wajen yin wannan yarjejeniya.
Daga cikin waɗanda aka ga fuskokin su akwai irin su Ado Aleiro ƴ an kuza da Kachalla Isiya Akwashi Garwa da Babaro wanda ake zargin ya jagoranci kisan massalata fiye da 30 a garin gidan Mantau a watan da ya gabata shine ya halarci taron.
- ’Yan Bindiga Sun Sako Ma’aurata A Katsina Bayan Karɓar N50m A Matsayin Kuɗin Fansa
- Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina
Shi dai wannan taron an gudanar da shi a ranar lahadin da ta gabata 14 ga watan Satumba, 2025 a garin Hayin Gada Bilbis bisa waru sharuɗa da aka gindaya.
A ɓangaren al’umma an samu halartar shugaban ƙaramar hukumar Faskari Hon. Surajo Aliyu Daudawa da Ɗan Majalisa dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar Faskari injiniya Sama’ila Mu’azu Bawa.
Sauran sun haɗa da Hakimin Faskari da kuma na Mai Ruwa da wakilan al’umma da masu riƙe da masarautar gargajiya da sauran al’umma.
Sai kuma ɓangaren ɓarayin daji inda aka samu halartar manyan jiga-jigan da suka kwarai wajen tada zaune tsaye a yankin Funtua baƙi ɗaya.
Mutane iri su Ado Aleiro Ƴan Kuza da Kachalla Hassan Sarkin Fulani Mai Taru da Kachalla Isiya Akwashi Garwa da Kachalla Sari da kuma Alhaji Abdullahi da sauran dakarun daji duk sun halarci wannan zaman sulhu.
Rahotanni sun bayyana cewa an cimma wasu sharuɗa kafin a kulla wannan yarjejeniya tsakanin al’ummar ƙaramar hukumar Faskari da kuma su shugabannin ƴ an bindiga kamar haka;
Su Fulani ko ɓarayin daji su daina kashe kowa ko sace jama’a domin yin garkuwa da su a nemi kuɗin fansa a ƙaramar hukumar Faskari
Sannan su Fulani sun amince kowa ya shiga daji ya yi aikin gona da kuma masu saran itacce ko zuwa zumunci a duk inda suke so an amince da haka sannan za su sako waɗanda suka yi garkuwa da su.
Suma a ɓangaen wakilan al’umma sun gindaya cewa an amince ɓarayin daji su shiga ko’ina a ƙaramar hukumar Faskari kamar yadda aba ake yi, amma ba tare da bindiga ko wani makami ba.
Kazalika an amincewa ɓarayin daji su ziyarci asibitoci domin duba lafiyar su ba tare da an tsangwame su ba, sannan su mayar da yaran su makarantar Boko
Abu na ƙarshe a cikin yarjejeniyar shi ne, an amincewa ɓarayin daji su cigaba da mu’amularsu ta yau da kullum kamar cin kasuwa, saye da sayarwa kamar kowa ba tare da wata fargaba ba.
Al’ummar da wannan iftila’i ya shafa sun amince da wannan yarjejeniya wanda suka ce ita ce hanya guda ɗaya da ta rage masu domin su zauna lafiya su da iyalansu.
Wasu kuma na sukar wannan sasanci da cewa to yanzu ina makomar waɗanda aka zalunta aka kashe masu ƴ an uwa da ɓarnata masu dukiyoyi? Suma a bangaren ɓarayin daji sun koka da irin ɓarnar da aka yi masu.
Fatan da ake da shi yanzu shine idan haka zai zama maslaha tsakanin al’umma da kuma ɓarayin daji to Allah ya tabbatar da ɗorewar lamarin a jihar Katsina da arewacin Nijeriya baƙi ɗaya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp