A yau Juma’a, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani mai taken “Nasarar Aiwatar da Manufar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) a jihar Xinjiang a Sabon Zamani”.
Takardar ta nanata cewa, jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin bisa jagorancin Xi Jinping, ta aiwatar da manufar tafiyar da harkokin Xinjiang, wadda ta ke jagorantar ayyukan Xinjiang na daukaka kirkire-kirkire a cikin yanayi mai sarkakiya, da samun nasara yayin da ake fuskantar hadurra da kalubale, da cimma manyan nasarori da sauye-sauye a dukkan bangarorin raya jihar.
Takardar ta kuma bayyana cewa manufar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a Xinjiang a sabon zamani ta samu hanya mai dacewa, ta daidaita harkokin raya jihar, da na tsaron iyaka, da karfafa ayyukan zamanantar da kasar Sin a Xinjiang, da cimma burin wanzuwar zaman lafiya mai dorewa da kwanciyar hankalin al’umma a jihar.
Har ila yau, takardar ta bayyana cewa a bana ake cika shekaru 70 da kafuwar jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. Kuma ba makawa, karkashin manufar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, hanyar raya jihar Xinjiang za ta kara fadada, kuma makomar jihar za ta kara haske. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp