A yau Juma’a ne aka rufe taron dandalin tattauna batun tsaro na Xiangshan karo na 12 a birnin Beijing, bayan mahalartansa sun zurfafa tattaunawa karkashin jigon “Mara baya ga odar kasa da kasa da ingiza ci gaba cikin lumana.”
An bude taron ne a ranar Laraba, ya kuma hallara sama da wakilai 1,800, ciki har da jami’an gwamnatoci, da kwararru, da masana da wasu masu sanya ido daga kasashe, yankuna da hukumomin kasa da kasa sama da 100.
Mahalarta taron, sun zanta karkashin jigo daban daban, ciki har da “Gina tsarin adalci da daidaito na shugabancin harkokin tsaron kasa da kasa,” da jigon “Amincewa da juna bisa matsayin koli da hadin gwiwar tsaro a yankin Asiya da Fasifik”. Sai jigon “Odar kasa da kasa da tsaron duniya da samar da daidaito,” da kuma “Gina zaman lafiya na shiyyoyi karkashin tsarin tattaunawa da gudanar da shawarwari.”
Taron ya kuma bayar da damar tattaunawa tsakanin manyan kwararru, da dakarun sojoji da malamai, kana an gudanar da wasu tarukan karawa juna sani na sirri, wanda hakan ya ingiza musayar koyi da juna, da fadada kafofin tattaunawa tsakanin Sin da mahalarta tsaron na sassan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp