Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu.
Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna, da tabarmi, da gidajen sauro, da magungunan zazzabin cizon sauro.
A cewar ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai, kimanin mutane 273,000 ne ambaliyar ta shafa a gundumomi 12 na jihohin Jonglei da Unity da Upper Nile da Central Equatoria, inda jihohin Jonglei da Unity suka dauki sama da kaso 91 na jimilar mutanen da ambaliyar ta shafa.
Martha Remijo Rial, daraktan kula da harkokin Sin a ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta ce gudunmuwar wata alama ce ta hadin kai da abota dake tsakanin Sudan ta Kudu da Sin. Ta kara da cewa, burin kasarta shi ne, karfafa dangantaka da Sin a bangarori da dama. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp